Za’a samu tsaro idan muka kawar da bambancin dake tsakaninmu – Buhari ga yan Najeriya

Za’a samu tsaro idan muka kawar da bambancin dake tsakaninmu – Buhari ga yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa burinsa na tabbatar da tsaron Najeriya ta hanyar dabbaka tsare tsare da wasu shirye shirye masu muhimmanci ba zai yi tasiri har sai yan Najeriya sun kawar da bambancin dake tsakaninsu, sun hada kai da juna.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin wasu manyan yan Najeriya a fadar gwamnati Aso Rock Villa a ranar Alhamis, wadanda suka samu lambar girmamawa ta kasa yayin da suka kai masa ziyara.

KU KARANTA: Karya ta kare: Maigida ya kama matarsa a kwance da kwarto a kan gadonsa

Shugaban kasa Buhari yace akwai bukatar ganin yan Najeriya sun yi hubbasa wajen gudanar da ayyuka daban daban, saboda ta haka ne kadai za’a samar da ingantacce kuma yalwataccen tattalin arziki a kasa.

Don haka ya yi kira ga yan Najeriya musamman matasa dasu yi koyi da ayyukan da wadanda suka samu lambar girmamawan suka gudanar a kokarinsu na cigaba da gina kasar da kowanne dan Najeriya zai yi alfahari da shi.

Mutane 25 da kungiyoyi 7 ne suka samu wannan lambar girmamawa daga gwamnatin tarayya, daga cikinsu har da shugaban bankin UBA, Tony Elumelu, Alhaji Aliko Dangote, Oba Otudeko, Kanal Hameed Ali, Sam Omatsaye da sauransu.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Sai dai ya gargadi yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel