Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

Instagram ta sauke wata wallafa ta wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar mai sun Papi Chulo bayan da diyar gwamnan jihar Bauchi ta yi masa raddi mai zafi a kai.

An sauke wallafar ne bayan da mabiyan Fatima Zara Bala Muhammad suka kai kararsa a kan tsokacin cin zarafi da yayi ga Musulunci da Annabi Muhammad, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Komai ya fara ne bayan da Papi Chulo ya yi wallafa a kan hukuncin da aka yankewa Maryam Sanda. A lokacin musun, shi da wasu sun yi tsokaci a kan aure, saki da rawar da maza ke takawa a al'umma. Wasu daga cikinsu sunyi ikirarin cewa addinin Musulunci na goyon bayan tashin hankali, dukan mata kuma ba ya goyon bayan mata masu yin kwalliya.

Kalaman batanci ga musulunci a kan hukuncin Maryam Sanda - Diyar Gwamnan Bauchi ta yi martani
Kalaman batanci ga musulunci a kan hukuncin Maryam Sanda - Diyar Gwamnan Bauchi ta yi martani
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani da su kayi karatu tare da Maryam Sanda ya fadi irin halayenta da ya sani

A yayin mayar da martani a kan tsokacin, Zara ta kwatanta su da "masu shaidaniya da bakar zuciya" wadanda basu san komai ba game da dokokin Musulunci dangane da aure.

"Gaskiya ina matukar damuwa a kan makomar na bayanmu. Idan wadannan ne manyan gobe, toh akwai yuwuwar muna tunkarar barna ne. A kan me zaku taba addinin wasu? Mutane da yawa basu da tarbiya. Ina da 'yan uwa Kiristoci kuma kowanne addini yana koyar da jin kai da mutuntawa." In ji wani sassa na tsokacinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel