Wani da su kayi karatu tare da Maryam Sanda ya fadi irin halayenta da ya sani

Wani da su kayi karatu tare da Maryam Sanda ya fadi irin halayenta da ya sani

Wata mai suna Usman Rasheed a Twitter da ya yi ikirarin cewa sunyi karatun digiri na biyu tare da Maryam Sanda ya wallafa wani rubutu a dandalin sada zumunta kan irin rayuwar makaranta da su kayi da ba zai taba mantawa ba.

A cikin makon nan ne dai wata kotu da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samun ta da laifin kashe mijinta kuma uban 'yar ta, Bilyaminu Bello a shekarar 2017.

Bayan kotu ta yanke hukuncin kisar, ma'abocin amfani da manhajar da Twitter @sir_ussy, ya ce abin tausayi ne hukuncin da aka yanke wa Maryam na kisa inda ya kuma bayyana halayenta na kulawa da mutane da kyautatawa a lokacin da suke karatun digiri na biyu (MSc) a Dubai shekaru bakwai da suka gabata.

Ga wani sashi cikin abinda ya rubuta: "Abin bakin ciki ne yadda karshen Maryam Sanda zai kasance, na ba zan iya dena kallon hotunan da muka dauka a ranar da muka kammala karatu ba a Scotland kuma mun samu sakamako masu kyau. Ya Allah ka kare mu daga fushin da sai saka mu aikata abinda za muyi nadama. Allah ya kara rufa mana asiri."

"Har yanzu iya iya jin muryan Maryam Sanda tana cewa Master lokacin muna yi wa juna ba'a na kan ce mata 'yar Maiduguri/Gwoza. Innalillahi wa ina ilayhir rajiun. Abin babu dadi. Yara za su girma su ji abinda ya faru da iyayensu kuma za ayi ta kallonsu da abin har abada.

DUBA WANNAN: Yadda matar aure da kwartonta suka fatattaki mai gida daga gidansa bayan ya kama su suna lalata

"Ina tuna wa da Maryam lokacin da muke karatun MSc a Heriot Watt Dubai, duk lokacin da muka samu hutun rabin lokaci na minti 15 mu kan fita tare mu siya kayan kwalama mu ci. Mu kan yi hira da dariya mu koma aji..

"Abu mai wahala ne ganin wani da ka sani an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya...Lokacin muna Dubai mu kan tafi gidan Maryam Sanda a JLT/Marina ta dafa mana abinci. Maryam din da na sani shekaru 7 da suka gabata natsatsiya ce mai kula da mutane da riko da addini. Wannan karshe ne mara dadi a gare ta."

Wani da ya yi karatu tare da Maryam Sanda shekaru 7 da suka wuce ya fadi irin halayenta da ya sani
Wani da ya yi karatu tare da Maryam Sanda shekaru 7 da suka wuce ya fadi irin halayenta da ya sani
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel