Makaho ya saki matarsa bayan ya fara gani saboda wai mummuna ce

Makaho ya saki matarsa bayan ya fara gani saboda wai mummuna ce

- Wani magidanci wanda ya kasance makaho ya saki matarsa bayan ganinsa ya dawo

- Ya yi hakan ne domin a cewarsa bai san mummuna ya aura ba

- Wannan lamari ya sanya matar a tsaka mai wuya inda take neman shawara kan matakin da ya kamata ta dauka a kanshi

Wani magidanci wanda ya kasance makaho ya saki matarsa bayan ganinsa ya dawo kan cewa bai san mummuna ya aura a matsayin matar auransa ba.

A wani rubutu mai taba zuciya da aka wallafa a shafin zumunta yayinda ta ke neman shawara daga wata mai bayar da shawarwari kan aure, ta bayyana cewa mijin yana mata kallon bata da kyawun da zai sanya ta zama matarsa.

Makaho ya saki matarsa bayan ya fara gani saboda wai mummuna ce
Makaho ya saki matarsa bayan ya fara gani saboda wai mummuna ce
Asali: Facebook

Matar wacce aka bayyana a matsayin Cynthia ta yi bayyanin yadda lamarin yake a cikin wani dogon sako kamar haka:

"Sunana Cynthia kuma shekara ta 26. Na auri mijina don soyayyar da nake masa ba wai don kui ba. (Mu ba masu kudi bane amma muna da rufin asiri). Koda dai iyayenshi ne suka rokeni kan na aure shi, amma ina son shi.

"Na aureshi lokacin yana makaho kuma na dinga yawo wuri-wuri don nema masa magani saboda son da nake yi masa.

“Bayan shekaru biyu aka yi mishi aikin ido inda aka samu nasara. Da kudin da na aro daga kamfani na aka yi mishi aikin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa tsohon Antoni Janar, Mohammed Adoke, belin N50m

"Mako guda bayan ya fara gani sai ya bar gida sannan na samu labarin cewa yayi sabuwar budurwa wacce ya tare wajenta. Wata rana ya shigo gida ya bayyana kalaman da suka bani mamaki. Amma abunda ya ce mun shine ‘soyayya makauniya ce, wannan makantar ce tasa na auri mummunar mace. A yanzu idona biyu don haka ba zan zauna dake ba.’

"Me nayi wa wannan butulun da bai san halacci ba saboda na yanke shawarar mayar dashi yadda yake a baya, ina tunanin watsa mishi acid don in lalata halittar shi.

“Ina bukatar shawara, dan Allah."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel