Ka cancanci a daureka a kurkuku - Buhari ya mayar da martani ga Sanata Abaribe

Ka cancanci a daureka a kurkuku - Buhari ya mayar da martani ga Sanata Abaribe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani ga Sanata Eyinnaya Abaribe wanda ya yi kira da murabus dinsa a kan zarginsa da nuna halin ko in kula a kan tsaron kasar nan.

Idan zamu tuna, a ranar Laraba ne Sanatan yayi kira ga shugaba Buhari da ya yi murabus saboda halin da tsaron kasar nan ke ciki.

Amma kuma a martanin gaggawa da shugaban kasar yayi ta bakin mai bada shi shawara na musamman a kan yada labarai, Garba Shehu ya cewa kiran da Abaribe yayi na wawanci ne.

Kamar yadda shugaban kasar ya ce, kamata yayi a ce sanatan yana gidan Yari saboda kasa kawo shugaban IPOB, Nnamdi Kanu da yayi saboda shi ya tsaya ya karba belinsa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Takardar ta kara da cewa, "Kawai saboda wasu tsiraru na tunanin shugaba Buhari yayi murabus, sai kuma ya yi? Wannan ai ba ra'ayin 'yan kasar bane. Wannan ra'ayin shugaban 'yan kalubale ne wadanda suka saba irin wannan tsokacin.

Ka cancanci a daureka a kurkuku - Buhari ya mayar da martani ga Sanata Abaribe
Ka cancanci a daureka a kurkuku - Buhari ya mayar da martani ga Sanata Abaribe
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Duk kun rasa kujerunku' - PDP ta yi magana a kan mambobinta da suka koma APC a Imo

"Idan har akwai bukatar shugaba Buhari ya yi murabus, toh kuwa akwai miliyoyin 'yan Najeriya da ya kamata su yi murabus har da Sanata Abaribe wanda ya bude kofar tserewar Nnamdi Kanu.

"Shi yasa hannu har kotu ta saki Nnamdi Kanu da beli wanda daga nan ya gudu. Sanata Abaribe ya kasa dawo da shi kasar nan amma har yana da kwarin guiwar cewa wani ya yi murabus. Shi ya kamata a damke a matsayin wanda ake zargin.har sai ya kawo wanda ya sa hannun har ya gudu." cewar takardar.

Abaribe da jam'iyyarsa ne suka yi wa Najeriya fyade kuma suka barta a lalace a 2015. A halin yanzu Shugaba Buhari na gyarata ne amma suke koke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel