Shugabannin Kwakwasiyya na Kebbi sun koma jam'iyyar APC

Shugabannin Kwakwasiyya na Kebbi sun koma jam'iyyar APC

A ranar Alhamis ne shugabannin jam'iyyar PDP na darikar Kwankwasiyya, reshen jihar Kebbi suka koma jam'iyyar APC a jihar.

Shugaban matasan Kwankwasiyya na jihar, Mohammed I. Anaruwa Kele, wanda yayi magana a madadin masu canza shekar a Birnin Kebbi, ya ce hukuncin barin jam'iyyar ya biyo bayan tsananin biyayyarsu ne ga shugaban darikar Kwankwasiyya, Rabiu Suleiman Bichi.

Ya ce a lokacin da suka gano cewa shugabansu ya bar Kwankwasiyya, ba su kara wani tunani ba da ya wuce na komawa jam'iyyar APC din, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda yace, shugabannin Kwankwasiyyar sun amince da barin jam'iyyar ne ganin cewa burinsu da biyayyarsu ta ginu ne da ganin sun bada gudummawa wajen ci gaban damokaradiyya a jihar.

Kebbi: Ƙusoshin tafiyar Kwankwasiyya sun sauya sheka zuwa APC
Kebbi: Ƙusoshin tafiyar Kwankwasiyya sun sauya sheka zuwa APC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jama'ar Zaria sun maka rundunar sojin Najeriya a kotu

"Mun bar Kwankwasiyya ne saboda biyayya ga tsohon shugaban Kwankwasiyya, Rabiu Suleiman Bichi, wanda ya koma APC. Shugaba ne mai son ganin ci gaban damokaradiyya," cewar shi.

Shugaban APC na jihar, Bala Sani Kangiwa, ya karba masu canza shekar da hannu bibbiyu tare da sanar dasu cewa sun zama 'yantattun 'ya'yan jam'iyyar APC. Ya ce zai sanarwa shugabannin APC na dukkan kananan hukumomin don shirya yadda za a karbesu.

"A jam'iyyarmu, kowa daya ne. Bamu nuna banbanci. Daga yau kuna da damar taka rawa a jam'iyyar nan kamar yadda tsoffin 'yan jam'iyya zasu iya. Zamu gaggauta yi muku rijista tare da baku katin shaidar zama 'yan jam'iyyar," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel