Karya ta kare: Maigida ya kama matarsa a kwance da kwarto a kan gadonsa

Karya ta kare: Maigida ya kama matarsa a kwance da kwarto a kan gadonsa

Ke duniya, ina za ki da mu ne? wannan rayuwa irin na wannan zamani ya zama abin tsoro sakamakon yadda ma’aurata ke wasa da aure, basa rike mutuncin gidan aure, wanda hakan ke sabbab mace macen aure.

A nan ma wani magidanci David Ishaku ne ya bayyana ma kotu yadda ya kama matarsa zigidir haihuwar uwarta tare da wani katon kwarto a cikin gidansa, kuma ma a kan gadonsa, suna lalata da junansu, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Rundunar Sojan sama ta tura wani sabon jirgi yaki zuwa Maiduguri

David ya bayyana haka ne a gaban kotun shari’ar gargajiya da ke zamanta a garin Nyanya na babban birnin tarayya Abuja, inda yace matarsa Luciz ta gayyato wani kwarto cikin gidansa bayan sun rabu a kan ya yi tafiya.

Sai dai abin haushin ma shi ne koda ya kama malalatan biyu, sai dukansu suka hada hannu waken lakada masa duka, suka fatattake shi daga gidan, suka watsa masa kayansa, sa’annan suka garkame gidan a binsu.

“Na dana ma matata tarko ne kuma ta fada, saboda wata rana na yi tafiya ba tare da na fada ma matata ranar da zan dawo ba, isa na gida keda wuya sai na tarar ta kawo kwarto gida, amma da na yi mata magana, sai ta hada hannu da kwarton suka buge ni.

“Hakan ya matukar bata min rai, sai na ce ma matar ta fitan min daga gida, amma ta ki, sai ma watso min kayana ta yi waje sa’annan ta kulle kofa.” Inji shi.

Bayan sauraron David, sai Alkalin kotun, Shittu Muhammad ya bayyana cewa tun da Lucia bata halarci zaman kotun ba, kuma wannan ne karo na farko da aka gabatar da karar a gaban kotu, don haka ya daga sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Feburairu.

A wani labarin kuma, likitoci bakwai da ma’aikatan jinya biyar ne suke karkashin kulawa bayan an kebancesu a cibiyar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya dake garin Yola, babban birnin jahar Adamawa, sakamakon sun yi mu’amala da mutanen dake dauke da cutar zazzabin Lassa.

Wata mata mai dauke da juna biyu ne take dauke da cutar, sai dai bata samu nasarar haihuwa ba, inda ta yi barin cikinta, jami’an kiwon lafiya sun kamu da cutar ne a lokacin da suka kwantar da ita a sashin haihuwa, inda suka cire mahaifarta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel