Vanessa ta yi wa jama’a godiya bayan mutuwar Mijinta Kobe da Gianna

Vanessa ta yi wa jama’a godiya bayan mutuwar Mijinta Kobe da Gianna

Bazawarar da Kobe Bryant ya bari a Duniya, Vanessa Bryant, ta fitar da jawabinta na farko a Ranar Laraba bayan mutuwar Mijinta a Ranar Lahadi.

Vanessa Bryant ta yi magana ne ta shafinta na Instagram ta na godewa dinbin jama’an Duniya da su ka nuna mata so da kauna lokacin makoki.

“’Yan mata na da ni kai na, mu na so mu taya miliyoyin jama’an Duniya da su ka nuna mana ana tare da kauna a wannan mummunan lokaci.”

“Nagode da duk addu’o’inku, Mu na matukar bukatarsu.” Vanessa Bryant a Ranar Laraba.

“Mun yi matukar girgiza da wannan rashi kwatsam na Mijina da na ke kauna, Kobe – Mahaifin ‘Ya ‘yanmu, sannan da kuma ‘Diyata Gianna."

Miss Vanessa Bryant ta bayyana Marigayiyar ‘Diyarta Gianna a matsayin Mai tunani da abin ban mamaki, kuma abin kauna ga Natalia, Bianka da Capri.

KU KARANTA: Ya kashe ‘Danuwansa saboda ya gaji wayarsa ta IPhone

Tauraron Duniya Kobe Bryant da Vanessa Bryant wanda su ka yi aure a shekarar 2001 sun haifi Yara 4; Natalia, Bianka, Capri da Marigayiya Gianna.

Mai dakin Marigayin ta aikawa Iyalin sauran wadanda su ka mutu a jirgin ta’aziyyarta. “Babu kalmomin da za su iya misalta ciwon da mu ke ji.”

Bazawarar mai shekara 37 a Duniya ta bayyana cewa ta na taya Iyalin wadanda su ka riga ta gidan gaskiya tare da Mai gidanta, takaicin rashin.

“Ban san ya rayuwarmu za ta kasance bayan yau ba, kuma ba zai yiwu in iya tunanin rayuwa babu su ba. Kullum mu kan tashi da hasken Kobe da Gigi.”

Iyalin tsohon 'Dan kwallon kwandon ta kafa wata gidauniya domin agazawa Iyalin wadanda su ka mutu tare da Mijinta da 'Diyarta a hadarin jirgin saman.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel