Sarkin Karaye ya daga darajar mahaifin Sanata Rabiu Kwankwaso a masarautarsa

Sarkin Karaye ya daga darajar mahaifin Sanata Rabiu Kwankwaso a masarautarsa

Guda daga cikin sababbin manyan Sarakunan jahar Kano masu daraja ta daya, Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar II ya sanar da daga darajar mahafin tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

Daily Trust ta ruwaito jami’in watsa labaru na masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu yayin da yake ganawa da manema labaru a Kano.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An kama ‘kanwa uwar gami’ dake da hannu a kisan Janar Idris Alkali

Sarkin Karaye ya daga darajar mahaifin Sanata Rabiu Kwankwaso a masarautarsa
Mahaifin Sanata Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa mai martaba Sarki Ibrahim Abubakar II ya bayyana daga likafar mahaifin Kwankwaso, Alhaji Musa Saleh daga sarautar Majidadi zuwa Makama ya tabbata ne saboda muhimmancinsa tare da kokarin da yake yi na kawo cigaba a masarautar.

Biyo bayan wannan nadi, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso mai shekaru 99 ya zama guda daga cikin manyan yan fadan Sarki masu zaban Sarakunan masarautar Karaye. A shekarar 2000 ne marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya nada mahaifin Kwankwaso sarautar Majidadin Kano.

Idan za’a tuna a shekarar 2019 ne gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya nada sabbin manyan sarakuna 4 a jahar Kano, Karaye, Bichi, Rano da Gaya, wannan yasa Madobi ta fada a karkashin masarautar Karaye, kuma tuni mahaifin Kwanwkaso ya yi ma sabon Sarki mubaya’a.

A wani labari kuma, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana wasu manyan kalubale dake kawo tarnaki, tare da mayar da hannun agogo baya a yakin da Najeriya take yi da kungiyar ta’addanci na Boko Haram fiye da shekaru 10.

Zulum ya bayyana haka a ranar Talata, 28 ga watan Janairu yayin da yake gabatar da kasida a taron kara ma juna sani da kwalejin tsaro ta kasa ta shirya ma dalibanta na kwas 28 a babban birnin tarayya Abuja.

Zulum ya bayyana manyan matsaloli hudu da suka zamto kalubale ga yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas da suka hada da; cin hanci da rashawa, tserewar yan gudun hijira daga gidajensu, rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’a da kuma rashin kyakkyawan tsari.

“Kana bukatar abubuwan da suka dace domin kawo karshen yaki, makaman da suka kamata da sauran kayan aiki, amma a yanzu wani babban matsala shi ne rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’an gari, wannan babban matsala ne dake damunmu, akwai bukatar shawo kansa.

“Idan har jama’a basu koma garuruwansu ba, yakin ba zai kare ba, saboda akwai bukatar jama’a su koma gidajensu domin cigaba da al’amuransu na yau da kullum.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel