APC: Matawalle ya yi magana a kan dakatar da masu rike da sarauta a Zamfara

APC: Matawalle ya yi magana a kan dakatar da masu rike da sarauta a Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi martani a kan ikirarin jam'iyyar APC a kan dakatar da wasu masu sarautar gargajiya da yayi. Jam'iyyar APC ta ce hakan na da alaka da siyasa.

Kamar yadda rahoton da jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, APC ta yi ikirarin cewa an dakatar da Kanwa na masarautar Zurmi ne saboda ya tsaya a matsayin mai karbar belin shugabannin jam'iyyar da ke gaban kotu a kan matsalar tsaro na jihar.

Amma kuma, takardar da ta fita a ranar Talata, wacce mai bada shawara na musamman ga Gwamnan, Zailani Bappa ya fitar, ya ce abun kunya ne da APC ta danganta dakatar da basaraken da siyasa.

Kamar yadda gwamnan ya ce, kawai abin ya taso ne kuma ya zama dole a dakatar da basaraken a lokacin da aka ya karba belin shugabannin APC su biyu.

"Wannan zargi ne kawai da aka danganta da siyasa. An dakatar da basaraken ne saboda dalilan da suka hada da tsaro a yankinsa kuma cikakken bincike ne kawai zai iya wanke shi," takardar ta ce.

DUBA WANNAN: Himba: Kabilar da mata basa wanka amma da mace ake karrama bako

Takardar tayi kira ga jam'iyyar APC da ta guji irin wannan zargin a kan lamurran tsaron jihar tana mayar dasu wata hanya ta cimma burikanta na siyasa.

Takardar ta kara da cewa, "Jami'an jam'iyyar APC basu da wani muhimmancin da zasu jawo wani babban martani daga gwamnatin jihar.

"Gwamnan ya kara da alkawarin cewa mulkinsa ba zai kalmashe kafa yana kallon wasu jama'a suna hada karairayi masu matukar hatsari da sunan siyasa a jihar ba".

Takardar ta kara da kira ga jam'iyyar APC a jihar da ta kiyaye wajen abinda za ta ce ko aikata don har a halin yanzu shugabanninsu na gaban kuliya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel