Asara: Matashi mai shekaru 28 ya kashe mahaifiyarsa a Makurdi

Asara: Matashi mai shekaru 28 ya kashe mahaifiyarsa a Makurdi

Wani matashi mai shekaru 28 ya hallaka mahaifiyarsa a gidansu da ke kan hanyar zuwa kasuwar zamani ta garin Makurdi, babban birnin jihar Benuwe, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta rawaito cewa matashin, wanda ya yi kaurin suna wajen tayar da fitina a unguwarsu, ya kashe mahaifiyar tasa ne ranar Talata.

Shaidun gani da ido sun sanar da Daily Trust cewa matashin, kamar yadda ya saba, ya rufe 'yar uwarsa da duka a gaban mahaifiyarsu bayan cacar baki ta shiga tsakaninsu.

Mahifiyarsu ta yi saurin shiga tsakanin 'ya'yan nata bayan matashin ya ruga dakin girki ya dauko wata wuka domin yanka 'yar uwarsa.

Uwar tasu ta yanke jiki ta fadi a daidai lokacin da ta ke kokarin ganin matashin bai farka cikin 'yar uwarsa da wukar da ya dauko ba, kuma nan takke ta ce 'ga garinku nan'

Asara: Matashi mai shekaru 28 ya kashe mahaifiyarsa a Makurdi
Asara: Matashi mai shekaru 28 ya kashe mahaifiyarsa a Makurdi
Asali: UGC

Kafin mutuwarta, marigayiyar daliba ce da ke karatun digiri na uku (PhD) a jami'ar harkokin gona ta tarayya da ke Makurdi (FUAM).

DUBA WANNAN: Yahoo-Yahoo: Kotu ta yanke wa uwa da 'dan cikinta hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Benuwe, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai, ta ce matar da mutu tun kafin matashin mai suna Dominic ya taba ta.

Catherine ta bayyana cewa matashin yana tsare a ofishin rundunar 'yan sanda.

"Bayanan da muka samu na nuni da cewa matashin bai taba mahaifiyarsa ba kafin ta yanke jiki ta fadi. Takadarancinsa ne ya saka wa mahaifiyarsa ciwon da ya zama silar mutuwarta," a cewar Catherine.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng