Maganganu 4 masu muhimmanci da Sarki Sunusi ya fada ma Gwamna Ganduje

Maganganu 4 masu muhimmanci da Sarki Sunusi ya fada ma Gwamna Ganduje

Shugaban majalisar sarakunan gargajiyan jahar Kano, Sarki Muhammadu Sunusi II ya kai ma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ziyara kwanaki kadan bayan kotun koli ta tabbatar masa da kujerarsa ta gwamnan jahar Kano.

Sarki Sunusi ya kai ziyarar ne a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu tare da babban basaraken jahar Edo, kuma Sarkin Bini Omo N’Oba N’Edo Uku Akpolokpolo Ewurare II Eheneden Erediauwa, inda suka hadu da gwamnan a fadar gwamnatin jahar Kano.

KU KARANTA: Yansanda sun tarwatsa masu garkuwa a Katsina, sun kama miyagu 5

Sai dai a yayin jawabinsa, Sarkin ya yi wasu maganganu guda biyar masu muhimmanci kamar haka;

Maganganu 4 masu muhimmanci da Sarki Sunusi ya fada ma Gwamna Ganduje
Sanusi Ganduje
Asali: Twitter

- Sarki Ya taya Ganduje murnar samun nasara a kotun koli, inda Alkalan kotun suka tabbatar masa da halascin kujerarsa. A jawabinsa Sarkin yace: “Zan so na yi amfani da wannan dama a madadina da masarautata don yi maka murnar samun nasarar a kotun koli.”

- Sarki Sunusi ya sake yin kira ga kowa da kowa ya yarda da hukuncin Allah, kuma kowa ya rungumi duk yadda Allah Ya tsara hukuncinsa da hannu bibbiyu, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

“A matsayinmu na Musulmai, mun san cewa mulki na Allah ne, akwai bukatar Musulmi ya ajiye abinda ke ransa ya yarda da hukuncin Allah. Sa’annan ya wajaba a kanmu mu yi ma shuwagabanninmu addu’a.” Inji shi.

- Haka nan mai martaba Sarki ya bayyana manufarsa ta cigaba da baiwa gwamnatin jahar Kano goyon bayan game da duk wasu abubuwa da suka shafi samar da cigaba ga jama’a da jahar Kano gaba daya.

- Daga karshe Sarkin Kano ya bayyana muhimmancin hadin kai, inda yace ya saurari jawabin gwamna bayan samun nasara a kotun koli, inda kuma ya jiyo shi yana kira ga al’umma dasu hada kai, don haka shi ma ya kara jaddada hakan.

“Ina son na kara muryata a kan wannan na yi kira ga jama’a dasu hada kai, muna kira ga jama’a su ji wannan kira na hadin kai, su kuma bayar da hadin kan.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel