Barnar Abacha: FG zata kara karbar miliyan $321 daga wasu kasashe biyu

Barnar Abacha: FG zata kara karbar miliyan $321 daga wasu kasashe biyu

Gwamnatin tarayya ta kammala kulla yarjejeniyar yadda zata karbo dalar Amurka miliyan $321 daga kasashen Island of Jersey da Amurka.

A mako main gobe ne kasashen da Najeriya zasu rattaba hannu a kan yarjejeniyar dawo da kudaden, wadanda tsohon shugaban kasa a mulkin soji, Marigayi Janar Sani Abacha, ya barnatar a lokacin da yake karagar mulki.

An yanke shawarar karbo kudin ne yayin zaman majalisar zartar wa ta tarayya (FEC) wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranta a yau, Laraba.

Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya shine ya sanar da hakan yayin da yake magana a kan tattaunawar FEC dangane da kudin da Abacha ya barnatar.

Barnar Abacha: FG zata kara karbar $321 daga wasu kasashe biyu
Marigayi Sani Abacha
Asali: Getty Images

A cewarsa, an kulla yarjejeniyar dawowa da Najeriya kudin bisa fahimtar cewa tana bukatar kudi domin kammala babban hanyar Lagos zuwa Ibadan, gadar Neja ta biyu da kuma babbar hanyar Kaduna zuwa Kano.

DUBA WANNAN: Bincike: An gano yadda 'yan bindigar da suka addabi arewa ke samun makamai

Malami ya kara da cewa akwai karin wasu kudin, Yuro miliyan 6.8, da tsohon gwamnan jihar Delta, Mista James Ibori, ya barnatar da Najeriya ke son karbo wa daga kasashen ketare. Sai dai, ya ce har yanzu ba a fara tattauna a kan kudin da tsohon gwamnan ya barnatar.

Kazalika, ya bayyana cewa nan bada dadewa ba gwamnatin tarayya zata fara tattauna wa a kan yadda zata karbo dumbin dukiyar Najeriya da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison Madueke, ta barnatar,

Sai dai, Malami bai bayyana adadin kudin da gwamnatin tarayya ke saka ran karba ba a matsayin barnar Diezani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel