Jama'ar Zaria sun maka rundunar sojin Najeriya a kotu

Jama'ar Zaria sun maka rundunar sojin Najeriya a kotu

A ranar Laraba ne jama’ar yankin Gyallesu da ke karamar hukumar Zaria suka garzaya gaban wata babbar kotu mai daraja ta biyu don kai karar rundunar sojin Najeriya a kan kwace musu gonakinsu.

Sun kai karar shugaban rundunar sojin Najeriya, Yusuf Buratai, shugaban NMS Zaria, Mohammed Mukhtar-Bunza, Ministan tsaro, Bashir Magashi da ministan shari’a Abubakar Malami, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa jama’ar yankin sun yanke hukuncin kai karar gaban kotu ne bayan da suka zargi cewa an kwace musu gonar da suka gada tun daga kaka da kakanninsu.

A zaman kotun da aka yi a yau Laraba, 29 ga watan Janairu, Mai shari’a Dabo ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Maris.

Jama'ar Zaria sun maka rundunar sojin Najeriya a kotu
Jama'ar Zaria sun maka rundunar sojin Najeriya a kotu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC

A tattaunawar da aka yi da lauyan masu kare kansu, A. I. Omaji, ya ce sun bukaci a kara musu kwanaki kafin a fara shari’ar. Mai shari’a Dabo kuwa ya amince da hakan.

Lauyan masu kara ta bayyana cewa tuni kotu ta gindaya wa rundunar sojin Najeriya dokar hana karbar gonar daga jama’ar yankin Gyallesu din.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an dade ana rigima a kan wannan gonar wacce jama’ar yankin Gyallesu din suka ce sun gaje ta ne daga kakanninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: