Sunaye: Zulum ya nada 'yan jihar Anambra da Oyo a gwamnatinsa
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nada Kesta Ogualili daga jihar Anambra da Yusuf Alao daga jihar Oyo a matsayin masu bashi shawara ta musamman.
Ogualili, dan asalin karamar hukumar Dunokofia ne na jihar Anambra yayin da Alao dan asalin karamar hukumar Ogbomosho ta jihar Oyo.
Su biyun na daga cikin mutane 26 da gwamnan ya rantsar a jiya, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda gwamnan ya sanar, su biyun da ya nada wadanda ba ‘yan asalin jihar Borno din ba ya nada su ne saboda kwarewarsu kuma sun zauna jihar a shekaru aru-aru. Sun kasance masu ruwa da tsaki tare da goyon bayan jam’iyyar APC.
Gwamnan wanda mataimakinsa Umar Kadafur, ya wakilta, ya basu rantsuwar ofishin da aka ba kowannensu.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC
Ga jerin sunayen masu bada shawarar ta musamman gare shi:
1. Modu Mustapha
2. Ali Damasak
3. Mustapha Bulu
4. Hussaini Gambo
5. Bukar Busami
6. Tukur Mshelia
7. Tijjani Modu
8. Inna Galadima
9. Zarah Bukar
10. Mustapha Sandabe
11. Gadau Ngurno
12. Mohammed Maulud
13. Bole Kachallah
14. Abdulrahman Abdulkarim
15. Bashir Maidugu
16. Bukar Konduga
17. Umoru Gaya
18. Ali Zangeri
19. Tukur Ibrahim
20. Tijjani Kukawa
21. Abba Gubio
22. Malam Badu
23. Adamu Chibok
24. Ahmed Zarma
25. Kesta Ogualili
26. Yusuf Alao
Gwamna Zulum ya yi kira ga wadanda aka nada din da su dage don sauke nauyin da aka dora musu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng