Kaduna: 'N300 ba zata ciyar dani da 'ya'ya uku ba a rana' - Matar aure ta kai mijinta kara kotun Musulunci

Kaduna: 'N300 ba zata ciyar dani da 'ya'ya uku ba a rana' - Matar aure ta kai mijinta kara kotun Musulunci

Wata Malamar makarantar Firamare, Munira Muhammad, ta shigar da karar mijinta, Lawal Ibrahim, a gaban kotun Shari'ar Musulunci dake Magajin Gari a cikin garin Kaduna.

Munira ta shigar da karar Lawal ne domin neman kotu ta tilasta shi ya kara yawan kudin da yake bata tare da 'ya'yansu uku a matsayin kudin abinci kowacce rana.

Matar, wacce ke zaune tare da mijinta a cikin garin Kaduna, ta sanar da kotu cewa wasu lokutan Lawan yana bata kwano daya na nikakkiyar masara a matsayin abincinsu na ranar.

"N300 ba zata iya rikeni da yaranmu uku ba. Kotu tasha bamu damar mu koma mu sulhunta tare da bashi shawarar ya kara yawan kudin da yake bayar wa, amma ya gaza yin hakan. A saboda haka, ina neman wannan kotu ta raba aurenmu kawai," Munira ta fada cikin takaici yayin zaman kotun.

Kaduna: 'N300 ba zata ciyar dani da 'ya'ya uku ba a rana' - Matar aure ta kai mijinta kara kotun Musulunci
Kaduna: 'N300 ba zata ciyar dani da 'ya'ya uku ba a rana' - Matar aure ta kai mijinta kara kotun Musulunci
Asali: Twitter

Da yake kare kansa, Lawal, mai sana'ar tuka babur mai kafa uku, ya sanar da kotun cewa N300 da yake bawa iyalin nasa kullum, ta ishesu su ci abinci a rana guda tare da neman a bashi lokaci domin ya sasanta da matarsa.

DUBA WANNAN: Bincike: An gano yadda 'yan bindigar da suka addabi arewa ke samun makamai

Bayan sauraron kowanne bangaren, alkalin kotun, Murtala Nasir, gargadi Lawal a kan bukatar ya ji tsoron Allah, ya sauke nauyin iyalinsa da addinin Musulunci ya rataya a wuyansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel