Bincike: An gano yadda 'yan bindigar da suka addabi ke samun makamai

Bincike: An gano yadda 'yan bindigar da suka addabi ke samun makamai

A yayin da ake kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yayi murabus saboda tabarbarewar tsaro, wani bincike da cibiyar bincike ta 'Conflict Armament Research' ta bayyana yadda makamai suka samu hanya zuwa arewacin Najeriya.

A binciken da cibiyar ta gudanar a cikin shekaru uku da suka gabata, ta gano cewa mafi yawan bindigun da 'yan ta'adda dake amfani dasu a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara sun fito ne daga kasar Libya.

Masu binciken sun gano hakan ne bayan sun tantance daruruwan bindigun da aka samu ko aka kwace daga wurin 'yan bindigar da aka kama a jihohin uku.

A cewar binciken kungiyar, bindigun an kera sune a kasar Turkiyyya kuma suna da alaka da wani mutum da ba a ambaci sunansa ba.

Binciken cibiyar ya kara gano cewa kananan bindigun da 'yan ta'addar ke amfani dasu sun fito ne kasar Iraqi, kuma sune irin bindigun da masu ikirari a yankin Sahel ke amfani dasu.

Bincike: An gano yadda 'yan bindigar da suka addabi ke samun makamai
Wasu 'yan bindiga da suka shiga hannun jami'an tsaro
Asali: Facebook

Sai dai, cibiyar tace ba tana nufin cewa 'yan bindigar arewa nada alaka da kungiyoyin jihadi bane.

DUBA WANNAN: Sunaye: Buhari ya yi sabbi nade-nade a CBN, NCC da NCAA

A rahoton da cibiyar ta fitar, ta bayyana cewa akwai kwararan hujjojin dake nuna cewa wasu daga cikin makaman da 'yan bindigar arewa ke amfani dasu sun fito ne kai tsaye daga rumbun adana makamai na gwamnatin kasashen Libya da Iraqi, kamar yadda bincikensu ya nuna musu.

Yankin arewacin Najeriya yana fama da hare-haren 'yan bindiga dake tare manyan hanyoyin motoci ko kuma su kai hari kauyuka da wasu unguannin cikin birni tare da sace mutane domin yin garkuwa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel