Maryam Sanda za ta daukaka kara kan hukuncin kisan da aka yanke mata

Maryam Sanda za ta daukaka kara kan hukuncin kisan da aka yanke mata

Rahotanni sun kawo cewa Maryam Sanda, matar da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu kan laifin kasha mijinta za ta daukaka kara a kan hukuncin.

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa wani mamba na tawagar lauyoyinta ne ya bayyana hakan.

Justis Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ne ya yanke mata hukuncin kisa, bisa laifin kashe mijinta, Mista Bilyaminu Bello.

Sai dai kuma, wasu mata da masu rajjin kare hakkin dan adam sun yi Allah wadai da hukuncin kisan da aka yanke mata, inda suka bayyana hakan a matsayin mara karbuwa.

Amma wata mai neman yancin dan adam kuma jagorar tafiyar #BringBackOurGirls (BBOG), Misis Aisha Yesufu ta yi na’ am da hukuncin kisan, cewa bai iya hukuncin bane illa hakan ya nuna cewa an yi adalci a shari’ an.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da ita kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da kisan kai. A hukuncin da ya yanke, alkalin ya riki cewa bisa ga hujojjin da aka samu da shaidu da kuma jawabin yan sanda cewa ta yiwa mijinta mummunan suka da wuka har lahira a Abuja a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2017.

Maryam Sanda za ta daukaka kara kan hukuncin kisan da aka yanke mata
Maryam Sanda za ta daukaka kara kan hukuncin kisan da aka yanke mata
Asali: Facebook

Alkalin yayinda ya ke bayyana cewa an yanke hukunci ga mai laifin kamar yadda ya ke a sashi 221 na dokar da’a, wanda shine kisa.

“An bayyana cewa kada wanda ya yi kisa. Duk wanda ya kashe shima a kashe shi,” alkalin ya kara a cewa: “Maryam Sanda ta girbe abunda ta shuka. Jini ga jini ne.”

Sai dai kuma da yake martani ga hukuncin a jiya Talata, daya daga cikin lauyoyin, wanda ya nemi sakaya sunansa, ya bayyana cewa za su daukaka kara kan hukuncin.

“Tana da yancin da kundin tsarin mulki ya bata na daukaka kara kuma shakka babu ya zama dole ta yi aiki dashi,” inji shi, inda ya kara da cewa “dole za mu daukaka kara kan hukuncin.”

KU KARANTA KUMA: Karin VAT ba zai wani taba Talakan Najeriya ba – Shugaban Majalisa

Sanda ta kashe mijinta a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2017, ta hanyar caka masa wuka. An gurfanar da ita tare a mahaifiyarta da dan’uwanta. Sai dai kuma an sallami sauran saboda mai karan ya gaza nasabta su da tuhume-tuhumen.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel