Na biya dala biliyan 1 ($1b) domin samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka - Mawaki Akon

Na biya dala biliyan 1 ($1b) domin samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka - Mawaki Akon

- Shahararren mawaki Aliaune Damala Bouga wanda aka fi sani da Akon ya bayyana cewa ya dena sanya kayan karau masu matukar tsada

- Ya ce hakan ya biyo bayan halin da nahiyar Afirka ke ciki na rashin ababen more rayuwa da suka hada da wutar lantarki da ruwan sha

- Akon, wanda ya mayar da hankali wajen taimakon jama'a, ya ce ya zuba hannun jari dala biliyan 1 a China don samarwa da kasashen Afirka wutar lantarki

Mawaki Aliaune Damala Bouga wanda aka fi sani da Akon, ya bayyana dalilin da yasa ya dena saka kayan karau kwata-kwata, kamar yadda jaridar Newsbreak ta ruwaito.

Dan kasar Senegal din wanda a halin yanzu ya dage wajen taimakon jama'a, ya ce ya dena saka kayan karau masu tsada saboda ganin hakan ya ke a almubazzaranci. Ya ce 'yan Afirka na bukatar kayan more rayuwa wadanda suka hada da wutar lantarki da ruwan sha.

"Na saka hannun jarin dala biliyan daya a kasar China don samar da wutar lantarki a Afirka. Afirka na bukatar wutar lantarki, ruwan sha da sauran ababen more rayuwa wadanda har yanzu basu samu ba," ya sanar da wani gidan rediyon kasar Zambia.

KU KARANTA: Fasto na sayar da dan kamfe da rigar nono ga mata, wadanda zasu dinga jawo hankalin maza kansu

"Idan ka yi tafiye-tafiye ka ga abin tausayi, zaka so taimakawa. Sanya kaya masu tsada a yanzu basu gabana. Bana sa kayan karau yanzu. Na ga mutane masu tarin yawa mabukata kuma ina ganin laifin kaina idan na ziyarcesu.

"Saka dan kunne mai tsadar dala dubu hamsin ba shi bane. Kawai mutane ne zasu kalla kuma yayi musu kyau kuma su yaba. A don haka ne nake amfani da kudina don taimakon jama'a."

A cikin kwanakin nan ne Akon ya kammala yarjejeniyar gina birnin shi mai suna 'Birnin Akon' a kasar Senegal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel