Gwamnan Borno ya bayyana manyan kalubalen da ake fuskanta a yaki da ta’addanci

Gwamnan Borno ya bayyana manyan kalubalen da ake fuskanta a yaki da ta’addanci

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana wasu manyan kalubale dake kawo tarnaki, tare da mayar da hannun agogo baya a yakin da Najeriya take yi da kungiyar ta’addanci na Boko Haram fiye da shekaru 10.

Zulum ya bayyana haka a ranar Talata, 28 ga watan Janairu yayin da yake gabatar da kasida a taron kara ma juna sani da kwalejin tsaro ta kasa ta shirya ma dalibanta na kwas 28 a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da hauhawan matsalar tsaro a Najeriya

Gwamnan Borno ya bayyana manyan kalubalen da ake fuskanta a yaki da ta’addanci
Zulum
Asali: Facebook

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Zulum ya bayyana manyan matsaloli hudu da suka zamto kalubale ga yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas da suka hada da; cin hanci da rashawa, tserewar yan gudun hijira daga gidajensu, rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’a da kuma rashin kyakkyawan tsari.

“Kana bukatar abubuwan da suka dace domin kawo karshen yaki, makaman da suka kamata da sauran kayan aiki, amma a yanzu wani babban matsala shi ne rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’an gari, wannan babban matsala ne dake damunmu, akwai bukatar shawo kansa.

“Idan har jama’a basu koma garuruwansu ba, yakin ba zai kare ba, saboda akwai bukatar jama’a su koma gidajensu domin cigaba da al’amuransu na yau da kullum.” Inji shi.

Zulum ya cigaba da fadin cewa shugabanci a lokacin yaki ba karamin aiki bane dake bukatar aminci da jajircewa, don haka ya nemi a samar da tsare tsaren samar da daidaito, sake gina garuruwa da kuma mayar da jama’a gida, musamman bayan Sojoji sun kama yakin.

Daga karshe gwamnan yace a yanzu haka gwamnatinsa ta bullo da irin wannan tsari wanda za’a dauki tsawon shekaru 25 ana aiwatarwa. A wani labarin kuma, Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da hauhawan matsalar tsaro a Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Sai ya gargadi yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel