Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da hauhawan matsalar tsaro a Najeriya

Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da hauhawan matsalar tsaro a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

KU KARANTA: NEPA 2: Yadda wani matashi ya yi mutuwar ban tausayi a jahar Jigawa

Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da hauhawan matsalar tsaro a Najeriya
Buhari
Asali: Facebook

Sai dai Daily Trust ta ruwaito shi yana gargadi ga yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Buhari yace: “Na yi mamaki matuka game da abubuwan dake faruwa a yankin Arewa maso yamma, a lokacin da muke yaki da ta’addanci mun san akwai Boko Haram, amma abin dake faruwa a yanzu abin mamaki ne. wannan abu ya fi karfin addini ko kabilanci, manakisa ce kawai ake shirya ma Najeriya.

“Daga yanzu ya zama dole mu kara zafi a kansu, daga cikin aikin dake wuyar gwamnati akwai samar da tsaro, idan bamu samar da tsoro a kasar ba babu yadda zamu tafiyar da tattalin arzikin kasar”

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Femi Adesina a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, inda ya kara da cewa samun arzikin danyen mai a yankunan Benue, Bida, Bauchi da Gombe zai kara karfin tattalin arziki.

Tsohon gwamnan jahar, Babangida Aliyu, wanda ya yi jawabi a madadin tawagar ya zayyana ma shugaban kasa yadda ayyukan yan bindiga ya d’aid’aita jama’ansu, tare da fafattakar da dama daga muhallansu da gonakansu.

Sa’annan ya jinjina ma shugaban kasa bisa daukan matakai masu tsauri ta hanyar umarnin daya baiwa rundunar Sojan sama da ta kaddamar da hare hare da jiragen yaki a mabuyar yan ta’addan.

Shi ma a nasa jawabi, mai martaba Sarkin Bida, Alhaji Yahaya Abubakar ya tabbatar ma shugaban kasa Buhari goyon bayansu a gare shi a dari bisa dari, kuma ya yi addu’ar Allah Ya bashi kwarin gwiwa da basirar tafiyar da mulkin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel