Muna bukatar duk manyan motoci su bar hanyoyinmu - FG ta bawa direbobi wa'adi

Muna bukatar duk manyan motoci su bar hanyoyinmu - FG ta bawa direbobi wa'adi

Ministan aiyuka, Babatunde Raji Fashola, ya gargadi direbobin manyan motoci a kan ajiye motocinsu a gefen titunan gwamnatin tarayya.

Kazalika, Fashola ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bawa direbobin wa'adin kwanaki bakwai (mako guda) domin janye motocinsu daga duk titunanta.

Fashola ya bayyana hakan ne ranar Talata a ganawarsa da direbobin manyan motoci yayin ziyarar aikin titunan da FG ke gina wa a jihar Neja.

Ministan ya ce akwai bukatar direbobin su bar titunan tarayya, musamman wadanda ake aikin a kansu, domin bawa 'yan kwangila sukunin yin aiyukansu cikin tsanaki.

Muna bukatar duk manyan motoci su bar hanyoyinmu - FG ta bawa direbobi wa'adi
Fashola
Asali: Depositphotos

"Dole direbobin manyan motoci su kaurace wa wannan hanya, na baku wa'adin kwana bakwai kafin na kawo jami'an tsaro su fatattake ku.

DUBA WANNAN: Hukuncin kisa: Muhimman abubuwa a kan alkalin da ya yanke wa Maryam Sanda hukunci

"Muna so duk manyan motoci, NATO da kungiyar direbobi su bar hanyoyinmu, su nemi shingen ajiye motocinsu, su bawa 'yan kwangila damar kammala aikinsu a kan lokaci.

"Ku sanar da sauran direbobi su bar manyan hanyoyinmu, ya zama wajibi ku mallaki shingen ajiye motocinku, saboda matukar kuna barin motocinku a gefen hanya, 'yan kwangila ba zasu samu sukunin kammala aiyukansu ba," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel