Ba na so a kashe mata ta idan ta kashe ni, a kyaleta ta kula da yaranmu – inji baban soyayya

Ba na so a kashe mata ta idan ta kashe ni, a kyaleta ta kula da yaranmu – inji baban soyayya

Biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya a kan Malama Maryam Sanda, inda kotun ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kamata da laifin kashe mijinta, Biliyaminu, yan Najeriya sun yi ta tofa albarkacin bakunansu.

Yayin da wasu ke tausaya ma Maryam duba da yadda ta dinga kwararar da hawaye a gaban kotun har ma kamar za ta zauce, wasu kuma bayyana farin cikinsu suka yi saboda a cewarsu gaskiya ce kawai ta yi halinta.

KU KARANTA: Mun gamsu da kamun ludayin Gwamna Zulum – Jam’iyyar PDP

Ba na so a kashe mata ta idan ta kashe ni, a kyaleta ta kula da yaranmu – inji baban soyayya
Anenga da matarsa
Asali: Twitter

Sai dai ana cikin wannan musayar ra’ayi a tsakanin yan Najeriya, kwatsam sai wani matashi daga jahar Benuwe, wanda aka tabbatar likita ne mai suna Anenga Ushakuma Michael ya tayar da wata sabuwar kura da wani magana da yayi game da kisan miji a hannun mata.

Dakta Aneng cewa ya yi idan har abin Allah Ya kiyaye aka samu akasi har matarsa ta kashe shi, toh baya so a kasheta, ya fi so a kyaleta ta kashe banza, domin kuwa gara a barta ta koma gida ta kula da yaran da suka haifa.

Dakta Anenga ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda yace: “Na san matata sarai, ba zata taba kashe ni ba, amma idan wani ma yasa ta aikata hakan, a kyaleta ta cigaba da rayuwarta don ta kula da yarana.

“Ni ne nan Dakta Anenga Ushakuma Michael na rubuta wannan, kuma ina so a wannan ya zama shaida a gaban kotu cewa wannan ne matsayata.” Inji shi.

Likitan, wanda ya daura hotonsa da matarsa yana tayasu murnar cika shekaru 7 da aure bai tsaya nan ba, sai da ya kara da cewa: “Ina magana ne a kan matata, ba wai matar wani ba fa, idan ba zaka iya ma matarka wannan alkawari ba ina tausayinka, amma ina rokon a baiwa matata dama ta rayu, idan zai yiwu.”

Game da Maryam Sanda kuwa, zuwa yanzu tana can a daure a gidan yarin garin Suleja kamar yadda Alkalin babbar kotun tarayya ya bada umarni, inda za’a cigaba da riketa har sai lokacin daukaka kararta ya wuce, kafin a samu daman zartar mata da hukunci.

Idan har wa’adin daukaka karar ya wuce, shi ke nan sai a jira ministan Abuja, wanda shi ne kamar gwamnan Abuja ya bayar da umarnin kashe ta, idan kuma ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara, sai a cigaba da fafatawa a shari’ar har zuwa yadda hali ya yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel