Yara 10 zamu haifa da amaryata - Cewar Sulaiman angon Baturiya

Yara 10 zamu haifa da amaryata - Cewar Sulaiman angon Baturiya

- Kowa dai ya san irin yadda labarin Sulaiman da masoyiyarshi Janine ya karade lungu da sako na kafafen sadarwa

- Janine dai ta luluko tun daga birnin California na kasar Amurka ta zo har garin Kano wajen masoyinta da suka hadu a kafar sada zumunta ta Instagram

- Sulaiman da budurwar tashi sun bayyana burinsu na haifar yara guda 10 idan sunyi aure, a wata hira da suka yi da Daily Trust

Janine wacce ta yiwa birnin Kano tsinke a ‘yan kwanakin da suka gabata, ta zo ta iske saurayin nata, inda kuma ta bayyana cewa ita fa da gaske take auren shi za ta yi.

A cewarta ta yanke shawarar biyo masoyin nata ne, bayan taji zuciyarta ta gama aminta da shi, ta ce tayi soyayyar kafar sada zumunta da mutane da yawa, amma shi Isah soyayyar shi ta fita daban da sauran, kuma taji a ranta cewa da gaske yake yi.

Yara 10 zamu haifa da amaryata - Cewar Sulaiman angon Baturiya
Yara 10 zamu haifa da amaryata - Cewar Sulaiman angon Baturiya
Asali: Facebook

A wata hira da Daily Trust tayi da masoyan guda biyu, Sulaiman ya bayyana cewa yana so su haifi yara 10 ne da amaryarsa Baturiya, Janine Sanchez idan Allah ya yarda.

Tuna baya: Ganganci ne talaka ya auri mata hudu - Cewar Marigayi Sheikh Ja'afar

A cewar shi: “Ina sane da cewar ba yarinya bace, saboda haka ina ganin dan ta fini a haife hakan zai kawo mana matsala a soyayyar mu, ita dai soyayya babu ruwanta da tsufa ko yarinta; kuma hakan daya daga cikin Sunnah ta Annabi ce. A matsayina na Musulmi, Annabi yayi irin wannan a aurenshi na farko. Saboda haka ban tunanin hakan zai zama matsala a gareni.”

Da aka tambayeshi wanene zai zabawa yaran nasu addinin da za su yi, Isah ya ce, “Tambayar wane irin addini yaranmu za su yi wannan bata ma taso ba, tunda dai nine Ubansu, kuma nine shugaban gidan.”

Tuni mahaifin isa ya basu damar aure, inda aka sanya za ayi a watan Maris dinnan mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel