Tuna baya: Ganganci ne talaka ya auri mata hudu - Cewar Marigayi Sheikh Ja'afar
- Wani bidiyo da muka nemo na Sheikh Ja'afar yayi magana wacce ke da kamanceceniya da maganar da Sarkin Kano Muhammad Sanusi yayi
- Idan ba a manta ba Sarkin Kano yayi magan akan halin da yankin arewa ke ciki na talauci, inda ya alakanta hakan da yawaitar aure-aure da haihuwa da mutanen arewa ke yi
A makon da ya gabata ne muka fitar muku da wani rahoto akan Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, inda Sarkin yayi wata magan da ta kawo kace-nace a cikin al’umma.
Sarkin dai yayi magana akan yanayin al’adar ‘yan arewa ta auren mata da yawa da kuma yawan haihuwa barkatai.
Hakan ya sanya muka dan fadada bincike akan wannan magana ta Sarkin, inda muka ci karo da wani tsohon bidiyo na marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, inda yake magana akan ganganci da kuma kuskure a wajen talaka ya auri mace fiye da guda daya.
KU KARANTA: Gidan yari ne ya dace da matan da ke hana mazansu kwanciya dasu - Mzee Jackson Kibor
A bidiyon an jiyo Sheikh Ja’afar na magana kamar haka:
“Wannan shine sharadi, duk wanda ba zai iya yin adalci ba, ba zai aure na biyu ba, sannan bayan adalcin akwai batun ciyarwa.
“Duk kan mutumin da samun sa yana da karfin da zai ciyar da mace daya ne, albashinsa a wata, abinda yake samu a kasuwa, karfin jarinsa na iya rike mace daya ne. To a nan gurin kuskurene ya ce zai karo ta biyu, ya ce wai zai dogara ga Allah, yayi tawakkali ga Allah, wannan kuskure ne ba tawakkali bane, ganganci ne.”
Ga kuma takaitaccen bidiyon a kasa:
Idan ba a manta ba Sarkin ya bayyana cewa matukar nahiyar arewa za ta cigaba da zama da wannan al’adar ta aure-aure da kuma haifar ‘ya’ya da yawa to tabbas haka zamu cigaba da zama cikin talauci.
Sarkin dai yayi wannan magana ne a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a lokacin da ya halarci wani taro a jami’ar tarayya ta Gusau makon da ya gabata.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng