Bauchi: Saurayi mai kishi ya caka wa budurwarsa wuka saboda ta amsa kiran wani a gabansa

Bauchi: Saurayi mai kishi ya caka wa budurwarsa wuka saboda ta amsa kiran wani a gabansa

Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Juma'a a jihar Bauchi. Wani mutum mai bakin kishi wanda aka bayyana sunansa da Solomon ya soka wa budurwarsa mai suna Patience Zakarai wuka saboda ta dau wayar wani a gabansa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne wajen karfe 1:30 na dare a gidan wacce ta mutu dake yankin Gwallameji da ke tsakiyar birnin Bauchi.

Wata majiya da ta roki a boye sunanta ta sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa wacce ta rasun ta labarta masa yadda lamarin ya faru kafin ta ce ga garinku.

Ya yi bayanin cewa kowa ya san yadda budurwar da saurayin suke kaunar juna amma sun fara mugun fada ne bayan wacce ta rasun ta amsa wayar wani namiji tsakar dare.

Ya ce: "Ta bayyana min cewa komai ya faru ne wajen karfe 1:30 na dare a ranar Juma'a. Ta ce ta samu kiran wayar wani abokinta ne ba saurayinta. Lamarin ya fusata Solomon don ya fara fada mata miyagun maganganu. Ta yi kokarin yi masa bayani amma sai ya fara dukanta.

DUBA WANNAN: Maryam Sanda: Wata matar aure ta sake kashe mijinta a Katsina

"Ta fasa kwalba tare da buga masa a kai don kare kanta amma sai jini ya balle. Tuni ya dau wuka ya soka mata a baya. Da safiyar ne ya dauke ta ya kai ta asibiti inda aka dubata sannan aka dawo da ita gida duk da ta rasa jini mai yawa."

"Da yammacin ne naje dubata kuma ta bani labarin yadda abin ya faru. ban dade da tafiya ba kuwa aka sanar da ni cewa ta rasu bayan an mayar da ita asibiti."

Wata majiya mai suna Mercy Cirfat ta sanar da NAN cewa Solomon ya tsere bayan da ya ji wannan mugun labarin.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Kamal Abubakar ya tabbatar wa da NAN aukuwar lamarin. Ya ce an kama mai asibitin da ta rasu a wajensa. Ya kara da cewa za a kamo wanda ake zargin kuma zai fuskanci fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel