"Ni ba hotiho bane" - Mataimakin gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela
Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela a ranar Lahadi ya ce bai mayar da kansa hotiho ba a mulkin jihar. Tela ya sanar da cewa yana da rawar takawa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar.
Ya sanar da hakan ne ga manema Labarai a ranar Lahadi a Azare, babban birnin karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi.
Tela ya sanar da hakan ne a matsayin martani a kan cewa da ake mataimakan gwamnoni 'yan a bi yarima a sha kida ne don basu iya tsinanawa mutanen jihar komai.
"Ni ba dan kallo bane, ina da aiyuka kuma karara suke kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayyana. Toh a don haka ne nake ganin cewa mu bi kundin tsarin mulki ta yadda yake ba zamu samu matsala ba.
"Komai ya dogara ne da yadda mutum ya ke. Ko tayar gefe na da amfani. Idan mutum yayi faci a tsakar dare a dokar daji, a nan ne zai gane amfanin tayar gefe. Don haka zan ce ko tayar gefe na da amfani."
DUBA WANNAN: Ana tsangwamar budurwa a Jos saboda tayi kama da wacce ta fito a fim din batsa
Ya kara da cewa, "Muna ma'amala da sanatoci da gwamnooni tare da mataimakansu. Zan iya ce muku na je majalisar dattijai kafin gwamna na kuma yana mutunta ni saboda hakan. Hakazalika nima ina mutunta matsayinsa na gaba da ni a nan,"
Ya kwatanta Sanata Bala Muhammed a matsayin mutum mara matsala mai tsananin rashin girman kai wanda ke mulki tare da kowa.
"Ko da ya yanke hukunci kuma ya gano cewa kana da shawarar da ta fi tashi inganci, ya kan bada hakuri tare da daukar sabuwar shawarar," Tela ya ce
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng