Ana tsangwamar budurwa a Jos saboda tayi kama da wacce ta fito a fim din batsa

Ana tsangwamar budurwa a Jos saboda tayi kama da wacce ta fito a fim din batsa

Wani bidiyon wasu mata da aka yi fim din batsa da su a jihar Filato ya jawo cece-kuce a kafafen sadarwar zamani a makon da ya gabata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bidiyon na kunshe ne da wasu mata tsirara suna lalata da wani namiji mai suna Emeka wanda ya basu naira dubu talatain-talatin tare da alkwarin zai dinga basu dubu dari duk shekara.

Bayan bayyanar wannan bidiyon ne tashin hankali ya barke daga dangin wadannan ‘yan mata kuma aka dinga tsanagwamarsu cikin mutane.

Daya daga cikin wadanda wannan fim din batsan ya kawo wa matsala ita ce wata budurwa mai suna Amanda Mary Abel mai shekaru 23, wacce take zama a yankin Utan da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.

Ana tsangwamar budurwa a Jos saboda tayi kama da wacce ta fito a fim din batsa
Ana tsangwamar budurwa a Jos saboda tayi kama da wacce ta fito a fim din batsa
Asali: Twitter

Amanda ta sanar da wakilin jaridar Daily Trust yadda ake ta nuna ta tare da tsangwamarta saboda tayi kama da daya daga cikin ‘yan matan wannan fim.

DUBA WANNAN: Fim din batsa a arewa: Daya daga cikin 'yammatan faifain bidiyon ta kashe kanta

Ta ce da farko ba a fada gabanta sai dai a dinga guna-guni amma sai daga baya kakarta da wata innarta suka sanar da ita cewa an ganta a fim din batsa.

Tuni ta nemi fim din tare da daukar hoton yarinyar ciki wacce gefen fuskarta ce kadai ta fito, tare da hada shi da nata. Ta nuna wa mutane cewa tabbas akwai kamanni amma ba ita bace. Hakan kuwa bai sa an dena kyararta gami da tsangwamarta ba.

Kamar yadda ta ce, tana ji kamar ta kashe kanta sakamakon wannan tozarcin da take fuskanta

"Ina so kowa ya sani cewa ba ni ba ce a cikin fim din batsa. Mai kama da ni ce kawai. Sunana Amanda Mary Abel kuma ina zama ne a yankin Utan da ke karamar hukumar Jos ta Arewa. Ina rokon mutane da su gane cewa ba ni ba ce a cikin wannan fim din batsar, kamanni ne kawai.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel