Sarki Sunusi ya raka wani babban basaraken kudu zuwa wajen Ganduje

Sarki Sunusi ya raka wani babban basaraken kudu zuwa wajen Ganduje

Shugaban majalisar sarakunan gargajiyan jahar Kano, Sarki Muhammadu Sunusi II ya kai ma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ziyara kwanaki kadan bayan kotun koli ta tabbatar masa da kujerarsa ta gwamnan jahar Kano.

Sarki Sunusi ya kai ziyarar ne a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu tare da babban basaraken jahar Edo, kuma Sarkin Bini Omo N’Oba N’Edo Uku Akpolokpolo Ewurare II Eheneden Erediauwa, inda suka hadu da gwamnan a fadar gwamnatin jahar Kano.

KU KARANTA: Yan siyasan Najeriya za su samu karin albashi – Hukumar rarraba kudaden gwamnati

Sai dai Premium Times ta ruwaito sauran manyan sarakunan jahar Kano guda 4 sun riga isa fadar gwamnatin jahar Kano, don haka tafiyarsu bata zama daya da ta Sarki Sunusi ba, kamar yadda mai magana da yawun Ganduje, Abba Anwar ya bayyana.

“A yayin ziyarar da suka kawo fadar gwamnatin jahar, sabbin manyan Sarakunan hudu sun gaisa da gwamnan daban daban, inda Sarkin Karaye, Ibrahim Abubakar II ya fara gaisawa da gwamnan, sai Sarkin Rano, Tafida Abubakar-Ila.

“Sai Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir, wanda ya samu wakilin Sarkin Yakin Gaya, Wada Aliyu, daga karshe mai martaba Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero ya shiga suka kaisa da gwamnan. Dukkanin Sarakunan sun taya gwamnan murnar nasarar daya samu a kotu.” Inji shi.

Hazalika Sarakunan sun yaba da kokarin da gwamnan ke yi na shawo kan cutar zazzabin Lassa a jahar Kano. “Mun yaba da kokarin da gwamnatin jahar ke yi na shawo kan cutar Lassa, duba da kokarin gwamnatin, muna da yakinin an kusan shawo kan cutar.” Inji Sarkin Bichi.

A nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya bayyana godiyarsa ga Sarakunan, inda ya fara da yi ma marigayi Sarkin Kano Ado Bayero addu’a yana cewa: “Wannan ziyara ne mai cike da tarihi, wannan kujerar da ka zauna a kai, ita ce kujerar da mahaifinmu, marigayi Ado Bayero ya zauna a ziyarar daya kawo fadar gwamnati.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel