'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Mutanen garin Nkporo da ke jihar Abia sun yi wa wani magidanci dukan tsiya kuma suka banka masa wuta bayan ya bindige matarsa har lahira sakamakon 'yar rashin jituwa da ta shiga tsakaninsu.

Wata mai amfani da shafin Facebook da ta rubuta sakon ta'aziyya ga 'yar uwanta mai 'ya'ya shida mai suna Mercy Chichi, ta bayyana cewa matar da siya wa mijinta Kalu Ilum gida da mota kafin ya kashe ta.

Ta kuma bayyana cewa Mercy Chichi ta fadi cewa ta gaji da zaman auren saboda irin cin zarafinta da mijinta ke yi amma ta cigaba da zama da shi ne kawai domin 'ya'yan da suka haifa.

Rahotanni sun bayyana cewa Kalu ya shiga cikin rijiya ya boye bayan ya bindige matarsa a lokacin da ta ke shirya yara zuwa makaranta misalin karfe 7 na safiyar ranar Talata. Sai dai bayan ya fito, fusatattun mutanen garin sun masa duka har sai da ya mutu kuma suka kone gidansa.

'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota
'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Abin kunya: Siriki ya dirkawa amaryar mahaifin matarsa ciki

Eunice Ogbonna ta rubuta:

"Kanwa ta na tuna lokacin da ki ka zo gida shekaru biyu da suka gabata ki kace kin gaji da auren nan amma za ki cigaba da zama saboda 'ya'yan ki, Mercy Chichi Allah ya jikan ki, mutanen Nkporo za suyi kewan ki sosai."

Kalu gara ka dawo da dukkan abinda 'yar uwa ta ta yi maka, ta gina maka gida ta siya maka mota. Ba za ka taba samun kwanciyar hankali a rayuwar ka ba.

Daga bisani wani a dandalin sada zumunta Prince Dan Iyke ya wallafa a shafinsa cewa matasan Nkporo sun kashe Mista Kalu Ilum da ya bindige matarsa Mrs Chichi a safiyar yau.

Ya kara da cewa, ba za a taba manta irin bakin cikin da mutumin ya janyo wa garin na Nkporo ba da iyalan Misis Chichi amma dai haka rayuwa ta ke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel