Maryam Sanda: Wata matar aure ta sake kashe mijinta a Katsina

Maryam Sanda: Wata matar aure ta sake kashe mijinta a Katsina

Wata mata mai matsakaicin shekaru ta shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Katsina a karamar hukumar Malumfashi bayan zarginta da aka yi da sokawa mijinta wuka. A take kuwa ya sheka lahira.

Lamarin ya faru ne a kauyen Danjaku da ke karamar hukumar Malumfashi kamar yadda jaridar Katsina Post ta ruwaito.

Marigayin wanda aka bayyana sunansa da Malam Shamsu ya mutu ne bayan da aka garzaya da shi asibitin Galadima Abdullahi da ke Malumfashi.

Matar wacce har yanzu ba a gano sunanta ba an gano cewa ta halaka Malam Shamsu har lahira ne bayan da wata 'yar hatsaniya ta sarke tsakaninsu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da tabbatar da cewa an kama wacce ake zargin.

DUBA WANNAN: Rikicin sabbin masarautu: Yadda ta kaya a kotu a tsakanin dattijan Kano da Ganduje a ranar Litinin

Wannan na faru ne jim kadan bayan da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta halaka mijinta Bilyaminu Halliru har lahira.

Kotun ta kama Maryam da laifin kashe mijinta kuma an tabbatar da dukkan tuhume-tuhumen da ake mata. Za'a ajiyeta a gidan kurkukun Suleja har ta gama daukaka kara.

Bayan Yusuf Halilu, ya kama Maryam Sanda, da laifin kashe mijinta, an yi wani gajeran rikici a cikin kotun. Alkali Yusuf Halilu na furta cewa an kama ta da laifin kashe mijinta, Maryam Sanda ta arce daga cikin akwatin mai laifi a kotu amma ma'aikatan gidan Kurkuku da kotun suka damkota.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel