Yadda rikicin kabilanci tsakanin Fulani da Tibabe ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3 a Taraba

Yadda rikicin kabilanci tsakanin Fulani da Tibabe ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3 a Taraba

Akalla mutane uku ne suka rasa ransu, tare da barnar makudan dukiya a yayin wani kazamar rikicin kabilanci daya barke tsakanin al’ummar Fulani da kabilun Tibabe a kauyen Pangari na karamar hukumar Bali na jahar Taraba.

Jaridar Punch ta ruwaito wani mazaunin garin mai suna Pius Gura ya bayyana cewa wani bafulatani ne ya shiga gonar wani manomi dan kabilar Tibi mai suna Dooior James, tare da shanunsa, amma a lokacin da manomin ya nemi a biyashi barnar da shanun suka yi masa, sai bahillacen yasa adda ya kashe shi.

KU KARANTA: Boko Haram: Yan kunar bakin wake sun kashe mutane 3 a Masallaci a Borno

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mazaunin garin yana cewa bayan yan uwan manomi Dooir sun samu labarin abin day faru ne sai suka tattara kansu, inda suka kai ma bahillacen harin ramuwar gayya, suka kashe shi, daga nan ne lamari ya ta’azzara.

“Duk a wannan rana (Lahadi), da misalin karfe 6 na yamma ne sai yan uwan bafulatanin suka yi gangami suka kaddamar da farmaki a kauyen manomin, inda suka sake kashe mutum daya, sa’annan suka kona gidaje da dama.” Inji Gura.

Da yake tabbatar da harin, shugaban karamar hukumar Bali, Prince Musa Mahmood ya bayyana lamarin a matsayin abin tir da Allah wadai, sai dai yace hankula sun kwanta a yanzu sakamakon tura jami’an tsaro zuwa garin.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai mummunan farmaki a unguwar Kwatas na karamar hukumar Bokkos na jahar Filato inda mutane da dama suka mutu.

Gwamnan jahar Filato, Simon Bako Lalong ya tabbatar da harin, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkuri da makiyan jahar ke yi don ganin sun mayar da lalata zaman lafiyar da aka samu a jahar, tare da mayar da hannun agogo baya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel