Tura ta kai bango: Buhari ya bada umarnin yi ma yan bindiga ruwan wuta a Neja, Kaduna da Zamfara

Tura ta kai bango: Buhari ya bada umarnin yi ma yan bindiga ruwan wuta a Neja, Kaduna da Zamfara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin ga rundunar Sojan saman Najeriya da ta yi amfani da jiragen yakinta wajen saukar da ruwan wuta a kan yan bindigan dake fakewa a dazukan jahohin Zamfara, Neja da Kaduna.

Kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar, inda yace shugaba Buhari ya bayyana hare hare da kashe kashen da yan bindiga suka yi a matsayin musifa ga kasa.

KU KARANTA: Har yanzu bamu samu kudin fara aikin jirgin kasa na Ibadan zuwa Kaduna ba – Amaechi

“Shugaba Buhari ya samu tabbacin cewa a yanzu da kurar bazara ke raguwa a sararin samaniya, jiragen yakin Soja zasu fara tashi domin kai ma yan bindiga da barayin shanu hari a yankin dajin Dogon Gona na jahar Neja.

“Saboda haka rundunar Sojan saman Najeriya ta shirya sansani a garin Minna na jahar Neja inda jiragen zasu dinga shan mai, domin daga nan zasu dinga lulawa dazukan domin kai hare hare.

“Haka zalika rundunar Yansanda reshen jahar Neja ta bayar da tabbacin aiki tare da Sojan sama ta hanyar amfani da nata jiragen wajen kai hare haren.” Inji shi.

Daga karshe Garba Shehu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta tare da taya al’ummar jahar Neja alhinin asarar rayuka da dukiyoyi da suka sakamakon hare haren yan bindiga, inda ya bayyana cewa ba za su mayar dasu saniyar ware ba.

Idan za’a tuna, a yan kwanakin nan ayyukan yan bindiga ya ta’azzara a wasu yankunan jahohin Kaduna, Neja da Zamfara inda suke kai hare hare a lokutta daban daban, sa’annan su kwashi dukiya tare da garkuwa da mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel