Zabe: Abdulmunin Kofa ya yi magana a kan kayen da ya sha a Kano

Zabe: Abdulmunin Kofa ya yi magana a kan kayen da ya sha a Kano

Tsohon dan majalisar wakilai, Abdulmumini Jibrin Kofa ya zargi cewa wasu manyan mutane masu fadi a ji a jihar ne suka yi masa taron dangi don kayar da shi a zaben maye gurbin da aka yi a jiya Asabar. Wannan lamarin ne kuwa ya ba Ali Datti Yako damar samun nasarar lashe zaben mazabar tarayya ta Kiru/Bebeji.

Duk da haka, Kofa ya ce ya karba kaddarar da ta same shi kuma zai cigaba da biyayya da kuma aiyukan ci gaban jam’iyyar APC a jihar da kuma kasar baki daya.

Kamar yadda takardar da Kofa ya mika ga manema labarai tace: “A zaben maye gurbi na Kiru da Bebeji da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Janairu, mutanen mazaba ta sun fito sun sauke nauyin da yake kansu amma kuma sai aka hana su zaben wanda suke so ta hanyar amfani da karfi a kowacce gunduma. A gari na Kofa da ke Bebeji ne kadai aka kasa wannan magudin.”

Ya ce, “mun san munyi nasara amma anyi mana magudi ne.”

DUBA WANNAN: Sokoto: PDP ta yi nasarar lashe kujeru 4 a zaben maye gurbi

Kofa ya kara da cewa, “A rumfuna da yawa ba a yi zabe ba. An kwace kuri’un ne kuma aka fitar da sakamako daga sama. Tashin hankula, dabanci da magudin da aka yi duk a bayyane yake.”

Ya zargi cewa jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zasu iya bada shaidar cewa an sanar da sakamakon zaben ne ba wai saboda abokin hamayyarsa ne ya samu kuri’u mafi rinjaye ba.

“Ina da tabbacin cewa wadanda suke da hakkin tabbatar da zabe na gari a jihar kuma suka yi akasin hakan, ba zasu samu natsuwa ba kuma su jiraci sakamako daga Ubangiji.

“A don haka ne na karba sakamakon zaben da hannu biyu kuma ina taya Aliyu Datti Ahmed murna don zai dasa daga inda na tsaya. Ina fatan aiki tare da shi da kuma bashi taimakon da duk ya dace a sabon nauyin da ya hau kanshi. Bani da niyyar kai kara a kan komai, dole ne in yi gaba.” Cewar Kofa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel