Sokoto: PDP ta yi nasarar lashe kujeru 4 a zaben maye gurbi

Sokoto: PDP ta yi nasarar lashe kujeru 4 a zaben maye gurbi

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana 'yan takarar jam'iyyar PDP a zaben maye gurbin da aka yi a ranar Asabar, a matsayin wadanda suka lashe kujerun Sokoto ta arewa/Sokoto ta kudu da kuma Isa/Sabon-Birni na majalisar tarayya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Alhaji Abubakar Abdullahi na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 68,985 inda ya kayar da Alhaji Bala Hassan na jam'iyyar APC mai kuri'u 42,433. Hakan ce kuwa ta bashi nasarar hayewa kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Sokoto ta arewa/ Sokoto ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa a mazabar tarayya ta Isa/Sabon-Birni, Sa'idu Bargaja na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 44,490 inda ya kada Alhaji Sani Aminu-Isa mai kuri'u 41,048.

DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi: PDP ta lallasa APC a Kaduna da Bauchi, inda APC ta yi nasara a Cross River

Mai magana da yawun hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Sokoto, Musa Abubakar, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadi, cewa wannan sakamakon ya fito ne daga dakin karbar sakamakon zabe na jihar baki daya.

Musa ya bayyana cewa, a kalla 'yan takara 59 ne suka nemi kujeru biyun da aka yi zaben maye gurbin na majalisar wakilan.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an yi zaben maye gurbin ne na kujerun majalisar wakilan jihar na Binji da Sokoto ta arewa da kuma kujerun tarayya na Sokoto ta arewa/ Sokoto ta Kudu da kuma Isa/Sabon-Birni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel