Zaben kujerar majalisan wakilai: Dan takaran PDP ya doke APC a Bauchi

Zaben kujerar majalisan wakilai: Dan takaran PDP ya doke APC a Bauchi

Hukumar gudanar da zabe ta kasa ta alanta, Auwal Jatau, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) matsayin zakaran zaben kujerar majalisar wakilan tarayya na mazabar Zaki a jihar Baichi.

Baturen zabe, Farfesa Ahmed Kutama, ya sanar da haka ne ranar Asabar a cibiyar tattara zabe a jihar Bauchi.

Farfesa Kutama ya alanta Jatau matsayin wanda ya lashe zaben ne bayan ya samu kuri'u 15,405 yayinda abokin hamayyarsa na All Progressives Congress (APC), Umar Tata, ya samu kuri'u 15,307.

A zaben ciki gibin da aka gudanar yau, dan takarar PDP, Auwal Jatau, ya samu kuri'u 782 yayinda na APC, Umar Tata, ya samu kuri'u 782.

An hada da kuri'un da suka samu a zaben 23 ga Febrairun, 2019, sanna aka sake lissafi kuma aka alanta mai rinjaye matsayin zakara.

Hukumar INEC ta gudanar da zaben ne bayan kotu ta fitittiki Umaru Tata kuma ta bada umurnin gudanar da sabon zabe a rumfunan zabe hudu a mazabar Zaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel