'Yan bindiga sunyi garkuwa da ma'aikacin zabe, sun kuma sace kayan zabe
- An samu inda aka yi tashin-tashina a zaben maye gurbi na jihar Cross River
- Wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikacin wucin-gadi na INEC
- Kwamishinan INEC na kudu-kudu, Mohammed Lecky ne ya tabbatar da aukuwar lamarin
Wasu 'yan bindiga sunyi garkuwa da daya daga cikin ma'aikatan wucin-gadi na hukumar zabe mai zaman kanta yayin da ake zaben maye gurbi a jihar Cross River. Maharan sun tarkata da yawa daga cikin kayyaykin kada kuri'un sunyi awon gaba da su. Jaridar The Cable ta ruwaito.
Kwamishinan zabe mai kula da yankin kudu-kudu, Mohammed Lecky, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar, 25 ga watan Janairu. Ya sanar da manema labarai yadda aka yi garkuwa da ma'aikacin wucin-gadin a hanyarsa ta zuwa mazabar Abi. Ya kara da cewa ma'aikatan wucin-gadin da aka yi garkuwa da su a hanyarsu ta kai akwatunansu duk an sako su.
Kwamishinan ya bayyana da cewa ma'aikatan sun hada da 'yan bautar kasa. Amma kuma hukumar 'yan sandan jihar ta tabbatar da cewa zabe na tafiya lafiya kalau a mazabar Abi/ Yakurr duk da sun tabbatar da cewa an kwace wasu takardun kada kuri'u da safiyar yau.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai wa fasinjojin jirgin kasa hari a Kaduna
Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, DSP Irene Ugbo ya ce zaman lafiya ya dawo yankunan da aka fara samun hatsaniya da safiyar yau.
Amma kuma Legit.ng ta ruwaito cewa zaben maye gurbin da ake yi a Essien Udim, Akwa Ibom ya zama wani abu daban bayan da aka rike wasu ma'aikatan INEC a cikin wata makarantar sakandire da ke yankin.
A yayin tabbatar wa da manema labarai aukuwar lamarin a ranar Asabar, 25 ga watan Janairu, Don Etukudoh, mai magana da yawun INEC din ya ce an tsare wasu jami'an hukumar a makarantar sakandire ta Independent da ke Ukana. Etukodoh ya ce: "Har yanzu ana nan tsare dasu."
Kamar yadda mai magana da yawun INEC din ya sanar, wani ma'aikacin INEC din da ya bukaci a boye sunansa ya ce "Wasu wadanda basu bayyana ko su waye ba amma ana zargin jami'an tsaron fararen kaya ne da sojoji sun tsare wasu ma'aikatan INEC. Sun kwace musu wayoyinsu don mun kasa samunsu. Amma daya daga cikinsu ya turo mana da sako ta waya cewa suna ta dangwale a kan kuri'un kuma an hana su amfani da card reader din."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng