Zaben maye gurbi a Sokoto: Jama'a sun yi tururuwar fito wa domin kada kuri'a

Zaben maye gurbi a Sokoto: Jama'a sun yi tururuwar fito wa domin kada kuri'a

Zaben maye gurbi na 'yan majalisu a Sokoto na tafiya yadda ya kamata tare da masu kada kuri'u da suka fito da yawansu a kananan hukumomin Sokoto ta kudu da Sokoto ta arewa a jihar. Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa ana zaben ne a don kujerun 'yan majalisun jihar.

Mai magana da yawun hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a jihar Sokoto, Musa Muhammad, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa sun dau ma'aikatan wucin-gadi har 2,500 don zaben maye gurbin..

Musa ya ce an raba kayayyakin zabe tun da safiyar yau Asabar kuma hukumar ta tabbatar da cewa ma'aikatan sun isa wajen aiyukan tun da safiyar yau.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, wanda ya zagaya akwatunan, ya ce masu zabe sun fito da yawa kuma kayan aiki sun isa rumfunan zabe tun kafin karfe 8 na safe.

Ana ta amfani da Card reader, ana tantancewa kuma ana ta kada kuri'u a akwatunan. An samu tsaro isasshe a wajen zaben.

Zaben maye gurbi a Sokoto: Jama'a sun yi tururuwar fito wa domin kada kuri'a
Zaben maye gurbi a Sokoto: Jama'a sun yi tururuwar fito wa domin kada kuri'a
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun yi awon gaba da miliyoyi a ofishin MTN

An gano cewa masu zabe na komai cikin lumana kuma mata ne suka fi fitowa don kada kuri'unsu.

Wani dan bautar kasa mai suna Ekong Anyekanem wanda ke jagorantar akwati mai lamba biyu na gundumar Maishanu B a Unguwar Rogo ya ce komai na tafiya cikin lumana da zaman lafiya.

Anyekanem ya ce an tsara layin mata daban da na maza yayin da masu nakasa da tsoffi ake basu fifiko.

Mai anguwar Gagi, Sani Umar Jabbi ya nuna gamsuwarsa da yadda zaben ke tafiya a yankin. Jabbi ya saka kuri'arsa ne a akwati mai lamba 3 da ke Marafa a Gagi, kuma yayi kira ga masu kada kuri'u da su kiyaye dokokin INEC tare da gujewa duk abinda zai iya kawo tashin hankali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel