Abin kunya: Siriki ya dirkawa amaryar mahaifin matarsa ciki

Abin kunya: Siriki ya dirkawa amaryar mahaifin matarsa ciki

Wani tsohon soja mai suna Akwange ya bayyana yadda mijin 'yar shi ya dirkawa amaryar shi ciki. Akwange ya auri amarya Priscilla ne bayan matar shi mai diya mace daya ta rasu. 'Yan uwan shi sun yanke shawarar ya kara aure ne don samun mai kula da Faith.

Ma'auratan sun kwashe shekaru 10 bayan auren amma babu haihuwa. Duk wani asibiti ko wajen maganin gargajiya da za a iya zuwa, Priscilla ta ziyarta, amma shiru ba haihuwa, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Daga bisani sai 'yan uwan Akwange suka fara hura mishi wuta a kan ya kori Priscilla don ya auro wata ko zai samu karin 'ya'ya.

Wani tashin hankali shi ke shafe wani don kuwa Faith diyar Akwange ta rasu bayan kwanaki kadan da ta haihu. Tunanin wanda zai rike jaririn ne yasa aka tura Priscilla don zama tare da mijin Faith mai suna Christopher Chori.

Bayan watanni Akwange ya samu wayar abokinsa inda ya sanar masa cewa ya ga Priscilla dauke da katon ciki a kasuwar Lafia da ke jihar Nasarawa.

Abin kunya: Siriki ya dirkawa amaryar mahaifin matarsa ciki
Abin kunya: Siriki ya dirkawa amaryar mahaifin matarsa ciki
Asali: Depositphotos

Gani ya kori ji: Hakan ne kuwa yasa Akwange ya wanke kafarsa ya garzaya Lafia. Zuwansa ke da wuya tarar da matarsa da katon ciki.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai wa fasinjojin jirgin kasa hari a Kaduna

A take ta zube tana rokonsa gafara. "Ka gafarceni, nasan cikin nan ba naka bane amma ba zan iya zubar dashi ba. Cikin Chori ne kuma shi ya ja hankalina har ya dirka min. Amma kuma na gane cewa ina haihuwa kuma ba zan zubar ba don shekaruna karuwa suke. Ina rokonka da ka rufa min asiri, tare da kareni daga wannan kunyar."

A bangaren Chori kuwa, ya ce matar sirikinsa ce ta ja hankalinsa kuma ya bukaci a zubar da cikin amma ta ki. "Na rasa da idon da zan dubi sirikina don ba yin kaina bane. Matarsa ce ta ja hankalina tare da ra'ayina."

Kamar yadda Akwange ya bayyana, "Da yanzu ne nake aikin soja, ba shakka zanyi amfani da bindigata don tarwatsa kawunansu. Amma a yanzu dai bana bukatar kara ganinta, zai fi idan ta zauna a wajensa. Shi kuwa na bar shi, alhakina ba zai bar shi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel