Tun ina dan karamin yaro nake da sha'awar shiga kungiyar Kannywood - Fitaccen Darakta Abubakar Maishadda
- Abubakar Maishadda babban furodusa ne a masana’antar Kannywood wanda ba ya jin zafin kashe kudi don shirya fim
- A zantawar da babban furodusan yayi da jaridar Daily Trust ya sanar da cewa ra’ayin shiga masana’antar ya fara tasiri a rayuwar shi ne tun yana karami
- Ya shiga masana’antar a 2012 amma kafin nan yana bin manyan daraktoci da suka hada da Dan azumi Baba, Ashiru Nagoma da Shariff Aminu Ahlan
Abubakar Maishadda furodusa ne a masana’antar fina-finan Hausa. Shine mashiryin fina-finan ‘Hauwa Kulu’ da ‘Mariya’ da sauransu. Maishadda ya bayyana cewa ra’ayin shi na shiga masana’antar kannywood ta fara ne tun yana karami. Ya kuma shiga masana’antar ne a 2012. Amma kafin nan yana bin manyan daraktocin masana’antar da suka hada da Dan azumi Baba, Ashiru Nagoma, Shariff Aminu Ahlan, Abba El-Mustapha da Rabi’u Sarki.
“Na fada masana’antar ne da taimakon Abubakar A.S Mai kwai kuma daga baya na hadu da Ibrahim Bala wanda shima darakta ne. Mun yi aiki tare har muka shirya fim mai suna ‘Ba Girma.’ A 2014 ne na hadu da Hafizu Bello wanda ya bani damar shirya fim dina na farko mai suna ‘Bincike’ a 2014.” Cewar Mai shadda.
KU KARANTA: Dalilin da ya sanya matan Hausawa ke tsufa da zarar sunyi aure
A lokacin da jaridar Daily Trust ta tambayi furodusan ko shi ne ya fara shirya fim din turanci, sai ya ce “a’a ba ni bane. Kabiru Musa Jammaje ne ya fara yin fim mai suna ‘There is a way’ sai ni kuma na yi ‘This is the way’. Daga nan ne na yi ‘In search of the King’ wadanda suka zama manyan nasarori gareni.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng