Boko Haram sun kashe mutane 10 a Borno

Boko Haram sun kashe mutane 10 a Borno

A kalla mutane goma ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka bace bayan harin da 'yan Boko Haram suka kai karamar hukumar Dikwa da ke jihar Borno a ranar Alhamis, cewar wata majiya daga cikin 'yan sintiri, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne wajen karfe 10 na safe a Lura kusa da Gajibo mai nisan kilomita 10 daga Dikwa. Wadanda abin ya ritsa dasu sun je samo itace ne.

Majiya daga 'yan sintirin ta ce: "Sun hari mutanenmu da suka je samo itace a kauyen Lura da ke da nisan kilomita 10 daga garin Dikwa".

Gawar mutane 10 aka tarar kuma an kwashesu tare da gano iyalansu a cikin Dikwa. "Mun birne su a sa'o'in farko na ranar Juma'a kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Amma kuma da yawan mutanen da aka hara sun bace. Wani daga cikin su da ya samu tserewa ya sanar da cewa, da yawan wadanda aka hara basu dawo gida ba kuma babu gawawwakinsu."

Boko Haram sun kashe mutane 10 a Borno
Boko Haram sun kashe mutane 10 a Borno
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An sake kashe kwamandan kasar Iran

A wani labari kuwa, 'yan bindiga sun kai wa matifiya hari a tashan jirgin kasa na Rigasa a Kaduna a ranar Juma'a 24 ga watan Janairu. Matafiyan suna shirin shiga motocin da za su kai su gidajensu bayan sun iso Kaduna daga Abuja ne kwatsam sai 'yan bindigan suka far musu.

Duk da cewa a tabbatar ko 'yan bindigan sun sace wasu daga cikin fasinjojin a halin yanzu ba, wata majiya daga hukumomin tsaro da ta zanta da The Cable ta ce matifyan sun bar motocinsu a bakin titi sun tsere cikin daji yayin harin.

Majiyar tsaron ta ce; "Lokacin da jirgin kasar da ya taso Abuja karfe 6.30 na yamma ya iso Kaduna misalin karfe 8 na dare. Wasu daga cikin fasinjojin sun karasa gidajensu amma wadanda suka yi kokarin shiga gari ta hanyar Rigasa zuwa Airport sun gama da sharrin wasu 'yan bindiga."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: