Babu yadda za’a yi mu zama yan ‘A bi yarima a sha kida’ – Sanata Ahmad Lawan

Babu yadda za’a yi mu zama yan ‘A bi yarima a sha kida’ – Sanata Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Sanatan Ahmad Lawan ya musanta zargin da wasu yan Najeriya ke ma majalisar dokokin Najeriya game da cewa ta zama yar amshin shata ga gwamnatin Buhari, ta yadda take baiwa duk bukatun gwamnatin Buhari goyon baya.

Lawan ya bayyana haka ne yayin da yake mayar jawabi a filin jirgin jahar Jigawa inda wasu kungiyoyin dake goyon bayansa daga yankin Arewa maso gabas suka tare shi tare da taya shi murnar sake zagayowar ranar haihuwarsa.

KU KARANTA: Da yan Najeriya sun zabi Atiku da basu shiga mawuyacin hali ba – Obasanjo

Daily Trust ta ruwaito mai magana da yawun Sanata, Ola Awoniyi ya bayyana cewa yan Najeriya basu fahimci kyakkyawar alakar dake tsakanin bangaren zartarwa da bangaren majalisa ba, don haka suke ganin majalisar ta zama tamkar yar amshin shata.

Sai dai Ahmad Lawan yace babu wata bita da kulli, sharri ko batanci da zata sa majalisa ta lalata kyakkyawar fahimtar juna dake tsakaninta da bangaren zartarwa kawai don wasu su ji dadi, matukar hakan zai amfani jama’a.

“Don kawai muna zaman lafiya da bangaren zartarwa baya nufin mun zama yan a bi yarima a sha kida, kuma ba zamu bari hakan ya kautar da hankulanmu ba, ai zuwa yanzu mun ga abin da majalisar yan amshin shata ta yi.

“Mun gabatar da kudurori masu muhimmanci ga cigaban kasa da dama cikin watanni 6, idan kuma zamu cigaba da samun wannan cigaba da irin wannan fahimtar juna, gwara mu cigaba a haka.” Inji shi.

Lawan ya kara da cewa zasu baiwa bangaren zartarwa duk wani goyon baya da take bukata don cigaban tattalin arziki, amma zasu tabbatar da an yi abin da ya kamata, tare da bin doka, don haka ba zasu saurara ba a duk inda suka an karya doka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel