Lawan ya bayyana matakin da za su dauka idan gwamnatin Buhari ta taka doka

Lawan ya bayyana matakin da za su dauka idan gwamnatin Buhari ta taka doka

Shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan ya ce abin mamaki ne a ce wannan majalisar dattijan ta hatimi ce kadai. Lawan ya sanar da hakan ne a yayin da wasu magoya bayansa suka yi masa maraba a filin jirgin sama na jihar Jigawa bayan dawowar shi daga kasar waje.

Shugaban majalisar dattijan ya ce a halin yanzu majalisar ta shirya don kawo ci gaba a rayuwar 'yan Najeriya. Ya kara da cewa 'yan majalisar zasu taimaka matukar suka ga shugabanni sun yi karantsaye ga doka.

"Kwata-kwata ba a fahimce mu ba ko kuma anyi mana muguwar fahimta ne. Idan muka ce muna aiki da zababbu don tabbatar da ci gaban kasar nan, sai ka ji wasu suna cewa kawai aikinmu buga hatimi," Lawan ya sanar ta bakin mai magana da yawunsa, Ola Awoniyi.

Lawan ya bayyana matakin da za su dauka idan gwamnatin Buhari ta taka doka
Lawan ya bayyana matakin da za su dauka idan gwamnatin Buhari ta taka doka
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa tsohon kwamishina hukuncin shekaru 19 a gidan gyaran hali

"Bari in sanar da ku, babu wani daukar hankali ko bacin suna da zai tarwatsa hadin kan da muke da shi don amfanar 'yan Najeriya wadanda suka zabe mu. Hakazalika, babu abinda zai hana mu kwarin guiwar aiyukan da zasu tabbatar da habakar kasar nan." ya kara da cewa.

"A matsayinmu na 'yan majalisa, babu yadda zamu amince gwamnati ta taka doka. Zamu tabbatar da cewa an yi abinda ya dace. Saboda muna son zaman lafiya, ba zai zama dalilin da zai sa mu bar gwamnati ta taka doka ba. Mun san abinda majalisar 'hatimi' za ta iya. Mun tsallake abubuwa masu yawa da suka hada da kalubale a watanni shida da suka gabata." cewar Lawan.

Lawan ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da yi wa majalisar kasar nan addu'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel