Da yan Najeriya sun zabi Atiku da basu shiga mawuyacin hali ba – Obasanjo

Da yan Najeriya sun zabi Atiku da basu shiga mawuyacin hali ba – Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa da yan Najeriya sun zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa a zaben 2019 da ya fi shugaban kasa Muhammadu Buhari kokari duba da halin da kasar take ciki a yanzu.

Jaridar Blueprint ta ruwaito Obasanjo ya bayyana haka ne yayin hira da aka yi da shi a gidan rediyon BBC Yarbanci inda yace tabbas Atiku Abubakar sai ya fi Buhari kokari da kwatanta gaskiya a matsayin shugaban kasa.

KU KARANTA: Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya sallami shuwagabannin tsaron Najeriya

“Abin da nake cewa a nan shi ne duba da halin da muke ciki a yau, idan ka dubi wadanda suke mulki a yau, har da ma shugaban namu gaba daya, na tabbata da Atiku Abubakar ne a mukamin da sai ya fi tabukawa.

“Atiku fa ba mala’ika bane, ya yi ma mutane da dama laifi, cikinsu har da ni kaina, amma kuma ya nemi gafara na, kuma na gafarta masa saboda koyarwar addini na, a matsayina na kirista, Ubangijina Yace na gafarta ma wanda ya yi min laifi, kuma abinda na yi kenan.

“Don haka lokacin da yazo wajena da malaman addinin kirista da islama yana rokon na gafarta masa, sai na ki gafarta masa, ni ubangiji ne? ba wai ina nufin halayensa na baya masu kyau bane, amma dukkanmi ajizai ne, ko akwai wanda bashi da laifi, idan akwai ya fito mu gan shi.” Inji shi.

Daga karshe Obasanjo ya nanata jawabinsa na cewa idan aka duba halin da Najeriya take ciki a yau, tabbas Atiku Abubakar sai ya fi kokari fiye da shugaban kasar yanzu, idan da shi ne ya samu irin wannan dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel