Kuda wajen kwadayi: Ta auri wani mutumi saboda kudin, daga baya yaje yana hada ta da karenshi yana lalata da ita

Kuda wajen kwadayi: Ta auri wani mutumi saboda kudin, daga baya yaje yana hada ta da karenshi yana lalata da ita

- Wata mata ta yi kira ga mata masu masifar son kudi da burin auren namiji mai tarin dukiya

- Ta bayyana yadda mijinta ya aureta don kawai Karen shi ya dinga saduwa da ita saboda arzikin shi na tsafi ya ci gaba da habaka

- Daga bisani kuwa mijin ya haukace inda ita kuwa likita ya tabbatar mata da mahaifarta ta lalace har abada

Wata mata ta yi kira ga 'yammata masu masifar son abin duniya tare da ganin auren namiji mai kudi ne kadai mafita. Ta fallasa yadda ta cuci rayuwarta a kan wannan dabi'ar ta ta.

Kamar yadda matar ta bayyana, tana tare da saurayinta wanda yake hidimar kasa amma sai ta ke ganin kamar bai isa aurenta ba ko kuma ba ta san lokacin da zai yi arzikin ba.

Bayan makonni biyu da rabuwa da saurayinta ne ta ci karo da wani hamshakin mai kudi. Ta bayyana cewa motocin shi uku kuma yana da katon gidan kan shi tare da abubuwan more rayuwa.

Sau da yawa ya kan je ya dauketa don yawon shakatawa tare da siyayya kala-kala.

A takaice dai sai maganar aure kuma aka yi aka kammala babu bata lokaci. A nan ne kuwa ta fara fuskantar kalubale.

KU KARANTA: Har yanzu ina nan ban yi bankwana da Kannywood ba - Hadiza Kabara

"Mun yi aure kuma muna zaman lafiya da mijina mai kudi. A rashin sani na ashe maganin bacci ya ke bani duk dare don kuwa bacci mai nauyi nake yi wanda ban sanin abinda nake yi. Wata rana da ya bani lemon, sai na nuna kamar na sha kuma har baccin ya dauke ni. Daga nan ya duba ni, ni kuwa na dinga minsharin karya. Yana fita sai ga shi da Karen shi sannan ya fara wasu sambatun sihiri. A take ya turo Karen wajena don ya sadu da ni. Ban san lokacin da na fara ihu cikin rudani ba."

Matar ta ce mijin ya roketa da ta rufa mishi asiri don kuwa wannan Karen ya aurar wa ita don shi ne silar arzikin shi. Idan bai sadu da ita ba mijin zai haukace.

Hakan kuwa ce ta faru don a ranar ya haukace bayan ta ki yadda Karen ya sadu da ita, kamar yadda jaridar Pulse ta wallafa

Daga baya ta je asibiti don a duba lafiyarta amma sai likita ya sanar da ita cewa mahaifarta ta lalace babu ita ba haihuwa har abada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel