Kwankwaso na shirin dawowa APC don takarar shugaban kasa a 2023 – Ganduje

Kwankwaso na shirin dawowa APC don takarar shugaban kasa a 2023 – Ganduje

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa cikin jam’iyyar APC domin cika burinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Daily Trust ta ruwaito Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya karbi tsohon sakataren gwamnatin jahar Kano, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi wanda yayi wankan tsarki ya koma APC daga gidan Kwankwasiyya a jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindiga sun sace shanu 105 a jahar Filato

A jawabinsa, Ganduje yace babban burin Kwankwaso shi ne ya tsaya takarar shugabancin kasar Najeriya, don haka ya bayyana shi a matsayin mutumin da bai san komai a siyasa ba, sai kyashi da hassada, ta yadda baya son ganin kowa a gaba sai dai shi kawai.

“Na san Kwankwaso fiye da kowa, mutum ne wanda ya fi kowa sani, ya fi kowa iyawa, mai son kansa, duk abin da zai umarceka ka yi toh ba don amfaninka bane, don bukatarsa ce, ina sane da duk dabarun siyasarsa da taurin kai, amma na jure iya tsawon shekarun da muke tare.

“Mutum ne wanda ba zai taba yaba ma duk wani abinda ka yi masa ba, walau babba ko karami. Wallahi a lokacin da muka tsaya takara a 1999 ni ne maigidansa, saboda ni na biya kudin fasta da tattara jama’a daga kananan hukumomi 44.

“Ni ne ma na ci zaben fidda gwani ba Kwankwaso ba, amma aka sulhunta mu, hatta mukamin mataimakin gwamnan ba Kwankwaso ya bani ba, haka na cigaba da biyayya a gare shi har lokacin daya zama minista na yi masa mashawarci.” Inji shi.

Daga karshe Ganduje yace bayan ya ci zabe a ya roki Kwankwaso ya bar masa sakataren gwamnati, kwamishinan sharia, mai magana da yawunsa da sauran jami’ai, sa’annan ya roke shi ya halarci taron rantsar da shi, amma yaki.

“Sai ya gwammace ya tafi Kaduna, haka nan na hakura, na kira shi a waya sau 9 don na ji ko ya isa Kaduna lafiya, amma bai dauki wayana ba.” Inji Ganduje.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel