Ile Arugbo: Iyalan Saraki sun nemi sulhu da gwamnatin Kwara

Ile Arugbo: Iyalan Saraki sun nemi sulhu da gwamnatin Kwara

Iyalan Saraki sun nemi kotu ta basu damar yin sulhu da gwamnatin jihar Kwara a kan batun IIe Arugbo.

Wasu lauyoyin na ganin wannan yunkuri ne da iyalan Sarakin su kayi na rufa wa kansu asiri saboda ba su da wasu takardu da ke nuna cewa sun saya filin lakadan kuma bisa kaida.

Bayan yin barazana da cika baki a kafafen yada labarai cewa filin na su ne, iyalan Sarakin sun garzaya kotu don gabatar da hujojji da wasu takardu da ke nuna cewa filin nasu ne.

Amma jamian kotu sun ce takardar kawai da iyalan Sarakin suka gabatarwa kotu ta hannun kamfaninsu Asa Investment Limited don nuna cewa filin na su ne wasika cewa ta bayar da fili a tare da wani satifiket na mallakan fili ba.

Gwamnatin jihar ta ce ainihi filin an ware shi ne don gina asibiti da sakatariyar jiha amma aka kwace shi da karfi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda ya ke cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 20 ga watan Janairun 2020 da aka aike wa Kwamishinan Shari'a kuma Attorney Janar na jihar, Barrista Salman Jawondo, lauyan kamfanin Barrista Ayodeji Ibrahim ya ce a shirye suke bawa alƙali dama ya huta domin su koma gefe suyi sulhu.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu sun cimma matsaya kan Amotekun

Lauyan Saraki ya kuma bukaci Kwamishinan Shari'ar ya yi amfani da "ofishin sa a matsayin babban jami'in Shari'a a jihar" domin ganin an tsayar da lokaci da wurin da za ayi zaman sulhun inda bangarorin biyu za su gana.

Wasikar ta cigaba da cewa, "Muna fatan za a duba bukatar mu a kan lokaci tare da bashi kulawar da ya dace muna aike wa da fatan alheri gare ka."

Da ya ke tabbatar da lamarin, babban sakataren yada labarai na gwamnan Kwara, Mr Rafiu Ajakaye ya ce gwamnatin jihar Kwara ta san da batun neman yin sulhun da iyalan Saraki suka nemi ayi.

Ya ce, An sanar da gwamnati abinda wasikar ya kunsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel