Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo NAjeriya daga Landan (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo NAjeriya daga Landan (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga Landan, kasar Ingila da daren Alhamis, 23 ga watan Junairu, 2020 bayan halartan taron alakar Birtaniya da nahiyar Afrika.

Hadimin Buhari kan soshiyal Midiya, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan ne a shafin na Tuwita.

Jirgin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Landan a ranar Juma’a, 17 ga watan Janairu.

Shugaban kasan ya halarci taron kasuwanci na Birtaniya da Afrika wanda ya gudana a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.

Firaye ministar Birtaniya, Boris Johnson ce ta shirya taron, sannan ana sanya ran zai hada shugabannin Afrika, manyan yan kasuwa na kasa da kasa, da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe dda kuma Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

A kwanakin da yayikasance a Ingila, shugaba Buhari ya gana da Shugaban kungiyar Commonwealth, Prince Charles a Glasgow, Scotland.

Shugaban kasar da tawagarsa sun gana da Firai minista Johnson da shugabannin wasu kungiyoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel