Sarki Sanusi ya bayyana abinda ke assasa rigima tsakanin Musulmi da Kirista a kasar nan

Sarki Sanusi ya bayyana abinda ke assasa rigima tsakanin Musulmi da Kirista a kasar nan

Mai martaba Sarki Kano, Muhammadu Sanusi II ya amince cewa jahilci ne ke assasa wutar gaba da rashin zaman lafiya da ke tsakanin Kirista da Musulmai a kasar nan.

A yayin bude taron zauren tattaunawa don zaman lafiyar addinai, Sarkin ya yi kira ga shugabannin siyasar kasar nan da su kare hakkin talakawa da kuma marasa galihu da suke mulka, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Sarki Muhammadu Sanusi II dai ya wakilci mai martaba sarkin Musulmi ne, Alhaji Sa'ad Abubakar III a taron.

Sarkin kano din ya ce sarakunan gargajiya da na addinai da ya kamata a ce su ne ke rike da akalar shugabannin siyasan an rufe musu baki sun yi mukus.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sojoji 8 a Borno

Idan dai ba zamu manta ba, Sarki Sanusi II na daga cikin sarakuna masu kira ga iyaye kan harkar ilimantar da yara domin su ne manyan gobe.

Ya kasance mai kira a kan tsaftace harkar almajiranci a kasar nan ko kuma ma barinta gaba daya.

A kwanakin baya ne mai martaban ya bayyana cewa almajiranci da iyaye ke tura yara kan gurbata musu tarbiya ta yadda suke tashi basu amfanar kansu balle jama'a.

Hakazalika 'yan siyasa na amfani da irinsu wajen cimma miyagun manufofinsu a yayin da suke neman kujerunsu ido rufe. Yaran kan kare a bangar siyasa, daba, sara suka da sauran miyagun dabi'u da zasu iya hana zaman lafiya a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel