Kotu ta wanke tsohon ɗan majalisa da ake zargi da kisan kai

Kotu ta wanke tsohon ɗan majalisa da ake zargi da kisan kai

Wata babbar kotun jihar Oyo ta wanke tsohon bulaliyar majalisar jihar, Olafisoye Akinmoyede, wanda ya wakilci mazabar Lagelu a majalisar jihar karo ta takwas a kan laifin kisan wani dan majalisar tarayya mai suna Temitope Olatoye Sugar.

An kashe Sugar ne a ranar 9 ga watan Maris na 2019 yayin zaben gwamnoni da na majalisar jihar a kauyen Alape dake yankin Lalupon, inda ya je kada kuri’arsa.

Kamar yadda majiyoyi suka sanar, wasu bata gari ne suka yi harbi wanda ya samu idonsa na hagu har ya bulla ta kansa.

Asibitin koyarwa na jami’ar jihar ne ya tabbatar da mutuwar dan majalisar bayan da aka gaggauta mika shi don karbar taimakon likitoci, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa, Sugar ya wakilci mazabun tarayya na Lagelu/Akinyele ne a majalisar wakilan kasar nan karo na takwas. Shi ne shugaban kwamitin majalisar a kan habaka birane da tsari.

DUBA WANNAN: Sokoto: Hukuncin kotun koli ba zai rage mu da komai ba - Wamakko

Olatoye yayi dan majalisar jihar daga 2011 zuwa 2015 kuma an zabesa don wakiltar yankinsa a majalisar tarayya a 2015.

Bayan aukuwar lamarin ne ‘yan sanda suka kama Akinmoyede da wasu mutane uku wadanda ake zargi da sa hannu a kisan kan kuma aka gurfanar dasu gaban kuliya.

Dan sanda mai gurafanarwa, M. A Ojeah, wanda ya wakilci kwamishinan jihar Oyo, ya zargesu da laifuka biyu da suka hada da kisan kai. Wadanda ake zargin kuwa sun musanta hannunsu cikin laifukan da ake zarginsu.

A yayin yanke hukunci a yau Alhamis, Mai shari’a Ademola Adegbola ya wankesu tare da sakinsu cewa masu gurfanarwar basu da wata shaida takamaimai da ke tabbatar da zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel